Ghana na daga cikin kasashen duniya da ke noma koko. Hoto/Reuters

Kasar Ghana ta kara kudin da za ta rinka biyan manoman koko da sama da kaso 63.3 cikin 100 ga manomanta.

Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin ke dauka na hana fasa kwabrin kokon zuwa kasashen makwafta inda ake sayar da shi a can.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana cewa manoman za su rinka samun cedi 20,943 wanda kwatankwacin dala 1,837 a duk tan guda.

Gwamnatin ta ce wannan karin zai soma a kakar kokon ta shekarar 2023/2024 wadda ke farawa a watan Satumba.

A baya dai gwamnatin kasar na biyan manoman koko cedi 12,800 a duk tan.

A yayin da yake magana a lokacin kaddamar da sabon farashin, Shugaba Addo ya bayyana cewa wannan shi ne farashi mafi yawa na koko da gwamnati za ta biya manoma koko a sama da shekara 50.

Wannan karin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin kokon ya karu a duniya, wanda shi ake amfani da shi wurin yin cakuleti.

Farashin na ta karuwa tun daga karshen watan Yuni, sakamakon cututtukan da tsirrai ke fama da su a Yammacin Afirka ciki har da cutar black pod.

Reuters