Gwamnatin Ghana ta hana fitar da kayan hatsi waɗanda suka haɗa da masara da shinkafa da waken soya na wani ɗan lokaci zuwa ƙasashen ƙetare saboda matsalar fari.
Ma'aikatar Noma ta ƙasar a ranar Litinin ta ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci a cikin gida a daidai lokacin da ƙasar wadda ke Yammacin Afirka ke fama da matsanancin fari wanda ya janyo koma-baya ga yawan amfanin gona a ƙasar.
Ruwan sama a arewacin Ghana ya yi ragu sosai a watanni biyun da suka wuce sannan idan aka kwatanta da bara ba a samu ruwan sosai ba.
Yanayin ranin da ake ciki a Ghana ya haifar da tsaiko a amfanin gona a ƙasa ta biyu da ta fi noman koko a duniya baya ga Cote d'Ivoire.
Kusan kadada miliyan 1.8 na gonaki ke fuskantar barazana, inda manoma suke noman abinci a kusan rabin yankin da lamarin ya shafa. Masara da shinkafa da gyaɗa da waken soya da dawa da gero da kuma doya ne suka fi fama da matsalar.
Manoman da matsalar ta shafa
Yankunan da matsalar ta shafa suna wadatar da Ghana kusan kashi 62 cikin 100 na hatsin da take nomawa a duk shekara, lamarin ya ƙara haifar da damuwa game da samun ƙarancin abinci a faɗin ƙasar, in ji Ma'aikatar Noma a wani taro da ta gabatar na manema labarai.
Dokar hana fita da hatsi za ta soma aiki ne nan-take kuma za a ci gaba da aiki da ita har sai lamura sun daidaita.
Ma'aikatar ta sanar da shirye-shiryenta na shawo kan matsalar ta hanyar amfani da albarkatun hatsi daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS), tare da ƙara shigo da hatsi daga ƙasashen waje, da haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.
Kazalika ta bayyana jerin ayyukan tallafi da za a yi don taimaka wa manoma da iftila'in ya shafa.
Sauyin yanayi
Ministan Kuɗi na Ghana, Mohammed Amin Adam ya faɗa a shafinsa na X cewa gwamnati na shirin tara dala miliyan 500 don samar da abinci.
Afirka na fama da yanayin zafi fiye da sauran ƙasashen duniya sannan yankin na iya jure tsananin sauyi da iftila'in yanayi kamar fari, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da kuma Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).
Gwamnatoci a nahiyar ta Afirka -- waɗanda da yawa daga cikinsu kamar Ghana, na fama da basussuka kana suna ƙoƙarin ganin sun samu kaso mai tsoka na kuɗaɗen tallafin yanayi na duniya a wannan shekara domin taimakawa wajen tunkarar barazanar da ake yawan fuskanta daga sauyin yanayi.