Kashin farko na aikin cibiyar ya kunshi kafa matatar mai da za ta samar da ganga 300,000 a kowace rana.

Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ƙaddamar da kashin farko na aikin cibiyar samar da albarkatun man fetur a ƙasar wanda zai ci dala biliyan 12.

A yayin ƙaddamar da aikin cibiyar wanda aka gudanar a ranar 19 ga watan Agustan 2024 a Nawule da ke gundumar Jomoro a yankin Yammacin ƙasar, Shugaba Akufo ya ce zai samar da sauyi a hanyoyin tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.

Wannan gagarumin aiki na sake fasalin yanayin makamashin Ghana ya biyo bayan yarjejeniyar dala biliyan 12 da gwamnatin ƙasar ta sanya wa hannu tare da gamayyar kamfanonin CP-UIC Consortium a farkon wannan shekara ta 2024.

Kashin farko na aikin cibiyar guda uku, ya ƙunshi kafa matatar mai da za ta samar da ganga 300,000 a kowace rana, da manyan injinan sarrafa mai wanda ya kai girman bpd 90,000 da kuma kubik mita miliyan uku na tankunan ajiya da tashar hanyar jiragen ruwa.

A jawabinsa, Shugaba Akufo-Addo ya ce aikin ya nuna irin haɗin gwiwa da gwamnati ke yi wajen ciyar da bangaren makamashin kasar gaba, ''a yayin da muka taru a nan don ƙaddamar da wannan aiki, mun ɗauki gaggarumin mataki na tabbatar da cewa dukkan gidaje da masana'antu a Ghana sun samu ingantaccen makamashi, mai rahusa kana wanda zai dace da yanayin muhalli,'' in ji shi.

Kazalika shugaban ya bayyana cewa, da zarar an kammala aikin, zai yi gogayya da da matatun mai da ake da su a Ghana da sauran yankin Afirka ta Yamma kamar matatar mai ta Tema (TOR) da Sentuo da kuma Dangote.

''Aikin zai samar da guraben ayyukan yi kai-tsaye ga mutum 780,00, sannan zai taimaka wajen daidaita kuɗin kasa tare da ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida da sanya Ghana a matsayin babbar cibiyar samar da man fetur da sinadaran fetur a Afirka,'' in ji Akufo Addo.

Don tabbatar da shirin samar da ma’aikata ‘yan kasar Ghana a cibiyar, shugaban ya bayyana cewa, ya umurci hukumar PHDC da ma’aikatar makamashi da su horas da ’yan kasar kusan mutum 200,000 waɗanda suke da ilimin boko a fannin da kuma dabaru da ƙwarewa.

TRT Afrika