'Yan majalisar Ghana sun ce akwai buƙatar siyasa mai karfi don cike gibin. / Hotuna: Getty 

Ghana na asarar dala biliyan 1.4 a kowace shekara saboda haramtattun kudade da kuma haraji da ake fitarwa daga ƙasar, a cewar mataimakin kakakin majalisar dokokin Ghana Joseph Osei-Owusu.

‘Yan majalisar sun hadu ne a ranar don kaddamar da kungiyar majalisar dokokin Africa kan haramtattun kudade da haraji (APNIFFT).

A yayin jawabinsa a taron Osei-Owusu, ya karanto binciken da kungiyar Justice Network Research ta gudanar.

"Idan muka ba da izinin fitar da kudade ba bisa ka'ida ba lokacin da bukatun jama'a ta taso, ko buƙatar saka hannun jari a kayayyakin more rayuwa, za mu kuka da kanmu domin za mu koma Neman rance Kuma ba za mu iya gudanar da ayyukan da suka kamata ba," in ji shi.

Kishi na siyasa

Osei-Owusu, ya kuma soki rashin kishin siyasa wajen aiwatar da dokokin da ke kare fitar da kudaden ba bisa ka'ida ba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Alexander Afenyo-Markin ya bukaci shuwagabanni da mambobin kwamitin da su fifita muradun Ghana tare da yin aiki don aiwatar da manufofin da za su rage fitar kudaden haram da kuma inganta ayyukan haraji.

An yi kiyasin cewa Afirka a matsayin nahiya za ta yi asarar kusan dalar Amurka biliyan 89 a duk shekara, sakamakon fitar da kudade haramtattu , a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

TRT Afrika