Hukumar Ƙididdiga ta Kasa a Nijeriya (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin farashin kudin saye da masu amfani da man fetur na PMS suka biya a watan Disambar 2023 ya kasance Naira 671.86 hakan na nuna karin kashi 225.85 cikin dari na duk shekara.
Hakan na kushe cikin rahoton da hukumar ta fitar a shafinta na intanet, inda ta ce idan aka kwantanta da watan Nuwamban 2023, an samu karin kashi 3.53 cikin 100 daga farashin N648.93.
''A binciken da aka gudanar na jihohi, an gano cewa, jihar Ogun ce ke kan gaba da mafi yawan farashin dillalan man fetur, a kan N776.54, sai kuma jihar Taraba da Adamawa da ke biye da ita akan farashin N760.00 da kuma N745.71, bi da bi,'' in ji Rahoton.
Kazalika rahoton hukumar ya yi kari da cewa “Jihar Kano da Lagos da kuma Borno suke da farashi mafi karanci na siyar da man Fetur din akan N602.78 da N612.72 da N622.71 bi da bi.
Daga bangaren shiyyoyi na kasar kuwa, shiyyar Arewa maso Gabas tana dauke da matsakaicin farashin sayar da man kan N699.82, yayin da shiyyar Arewa ta Tsakiya ke da mafi karancin farashin kan N657.69.
A bangaren farashin man Dizal kuma, wani rahoto da hukumar ta fitar ya nuna matsakaicin farashin man ya karu da kashi 37.76 cikin dari a tsawon shekara guda daga N817.86 da aka samu a cikin watannin farkon shekarar 2023 zuwa N1,126.69 kan kowace lita a watan Disamba 2023.
A duk wata, tun daga Nuwanba rahoton ya ce an samu karin kashi 6.74 cikin 100 daga N1,055.57 zuwa N1126.69 a watan Disamba 2023.