Farashin danyen man fetur ya fadi a ranar Alhamis sakamakon tasirin durkushewar da wasu manyan bankunan Amurka suka yi, da kuma karancin sayen man a kasuwannin duniya.
Bayanai na nuni da cewa farashin gangar danyen mai ya ragu daga dala 76. 67 zuwa dala 76.27 da safiyar Alhamis.
A lokaci guda kuma, an yi cinikin farashin danyen man fetur din a kasuwar Amurrka a kan dala 70.45 duk ganga daya, inda aka samu faduwar kashi 0.63 a kan farashin kasuwar na baya.
Hukumar Baitul Malin Amurka ta kara yawan adadin ribarta da kashi 25 duk da matsalolin da bankunan kasar ke fuskanta, da suka jawo rushewar bankuna hudu a cikin ‘yan makonni.
Shugaba Baitul Malin Jerome Powell a ranar Laraba y ace matsalolin da bankuna ke fuskanta a Amurka za su iya durkusar da kafatanin fannin idan ba a mayar da hankali a kansu ba.
An kara yawan danyen fetur din da Amurka ke sayarwa da ganga miliyan 1.1 inda jumullar ta koma ganga miliyan 481.2 a makon da yak are ranar 17 ga watan Maris, kamar yadda bayanan da Hukumar Sadarwa kan Makamashi ta kasar ta sanar a ranar Laraba.