Hamshaƙin kamfanin mai na Exxon Mobil Corp ya yi tayin zuba jarin dala biliyan $10 a harkar haƙar mai a gaɓar tekun Nijeriya, a wani shirin ƙarfafa zuba jari a ƙasar.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin kakakin fadar gwamnatin ƙasar, Stanley Nkwocha ranar Alhamis, inda ya ambato shuwagabannin kamfanin.
An sanar da batun zuba jarin ne yayin wata zantawa tsakanin mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima da shugaban kamfanin Exxon reshen Nijeriya, Shane Harris, a wani ɓangare na tarukan babban zauren MDD da ya gudana a New York ranar Laraba.
Exxon na shirin mayar da hankali kan gina filinsa na Owo project, wani ƙaramin shiri ne da ya kai dala biliyan $10. A halin yanzu kamfanin na Exxon Mobil Corp yana ayyukan haƙar mai a ƙarƙashin tekun Nijeriya.
Kamfanin haƙar man yana kuma shirin kashe dala biliyan $2.5 duk shekara don haɓaka man da yake fitarwa da ƙarin gangar mai 50,000 duk rana, cikin shekaru kaɗan masu zuwa.
Haka nan zai ci gaba da ayyukansa a Nijeriya, duk da amincewa da sayar da kadarorinsa na doron ƙasa ga Seplat Energy kan dala biliyan $1.3.
'Babban shiri'
An ruwaito Harris na cewa, "Exxon yana aiki tare da ofishin shugaban Nijeriya "don samar da kyakkyawan tsarin kuɗi da zai tabbatar da wannan babban shirin zuba jari."
Kakakin Exxon bai amsa neman ƙarin bayani da aka nema wajensa ba.
Samar da ɗanyen mai, wanda ke bai wa gwamnatin Nijeriya mafi yawan kuɗin shigan da take samu daga ƙasashen waje, ya ƙaru da kashi 10.15% cikin ɗari a watanni uku na farkon shekara, wanda ya kai ganga miliyan 1.41 duk rana, ƙari daga ganga miliyan 1.22 duk rana a bara.
Sai dai Nijeriya duk da ita ce babbar mai samar da mai a Afirka, tana fama da ƙalubalai a harkar manta, ciki har da yawan sata da lalata bututun mai. Hakan na faruwa duk da kafa dokar sauƙaƙa harkar zuba jari da saka-ido shekaru uku da suka gabata.
"Wannan zuba jari daga ExxonMobil ya dace da ƙudurin gwamnatin shugaba Bola Tinubu na mayar da Nijeriya wajen zuba jari cikin sauƙi," in ji Shettima.