Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya koma sayar da dala ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta daga ranar Alhamis.
Matakin CBN na zuwa ne a daidai lokacin da farashin naira ya sake faɗuwa zuwa 1,570 a kasuwar bayan-fage.
A yanzu haka, CBN ya koma sayar wa 'yan kasuwar canji kowace dala a kan Naira 1,450, kamar yadda sanarwar da ke ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan sashen kasuwanci da musayar kuɗi na CBN, AA Mahdi ta bayyana.
''Sakamakon sauye-sauyen da ake koƙarin samu a kasuwar canji da nufin samun daidaito a farashin canjin Naira, Babban Bankin Nijeriya ya lura da yadda ake ci gaba da samun rashin tabbas a kasuwar,'' in ji sanarwar CBN.
Yana ƙara da cewa ''hakan ya yi tasiri wajen ƙara ciyar da kasuwar canjin gaba tare da ƙara hauhawar farashin musayar kuɗin.''
"Don haka, CBN ya amince ya sayar da dala ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta don samun daidaito da kuma biyan buƙatun kasuwancinsu,'' in ji CBN .
Kazalika CBN ya ce ''za a sayar da dala 20,000 ga kowane ɗan kasuwar canji a kan N1,450.
Babban Bankin ya kuma gargaɗi 'yan kasuwar canjin da kar su ƙara ribar da ta wuce kashi 1.5 cikin 100 kan kowace dala da suka saya daga CBN ga masu hulɗa da su.
Dala, wacce aka sayar da ita a kan Naira 1670 a makon da ya gabata, ta farfaɗo zuwa 1,570 a kasuwar canji, inda a ranar Laraba aka rufe kasuwar a kan farashin Naira 1,565 kan kowace dala.