An dakatar da ayyuka a filin jiragen saman na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja na wani lokaci saboda hatsarin wani jirgin sama  / Hoto: Reuters

An rufe filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja na wani ɗan lokaci sakamakon hatsarin wani jirgi da ya sauƙa daga kan hanyarsa.

Lamarin ya faru ne bayan hatsarin wani jirgin kamfanin 'Allied Air ' da ke ɗakon kaya a babban filin jiragen saman na ƙasa da ƙasa a safiyar ranar Laraba, kamar yadda hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta fitar.

An ceto fasinjoji biyar da ke cikin jirgin kuma an garzaya da su asibiti.

An dakatar da ayyuka a filin jiragen saman na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja na wani lokaci, lamarin da ya haifar da jinkirin tashin jirage, kamar yadda rahotanni daga Nijeriya suka bayyana.

“Tawagar bayar da agajin gaggawa ta filin jiragen ta isa wurin tare da ma'aikatan binciken haɗura.

"An dai rufe hanyar tashin jiragen kana ana sa ran sake buɗe tashar nan ba da jimawa ba, '' a cewar mai magana da yawun hukumar FAAN Obiageli Orah a wata sanarwa da ta fitar.

Hukumar FAAN dai ta gargadi jama’a da su guji labaran ƙarya kan lamarin har sai a Hukumar Bincike kan tsaro ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahoto.