Darajar Naira ta fara farfadowa a cewar masana.

Kungiyar Kafafen Yada Labarai da Manufofin Gwamnatoci (IMPI) ta bayyana cewa akwai alkaluma tabbatattu da ke nuna tattalin arzikin Nijeriya na bunkasa kuma na jan hankalin masu zuba jari a karkashin gwmanatin Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwar da Kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta Niyi Akinsiju ya ce kungiyar ta su bayan nazarin da ta gudanar kan kasashen Nijeriya, Ingila da India ta kammala fitar da sakamako.

“Idan aka kwatanta da sanarwar Kungiyar Masu Samar da Kayayyaki ta Nijeriya da ke cewa daga cikin kamfanoni 767 d aaka rufe a 2023, wanda lamari ne da zai iya tunzura jama’a da jefa su cikin halin ha’ula’i, a Ingila kuma a daidai wannan lokaci an samu rufewar kasuwanci 345,000, wanda wannan ne karo na farko da a cikin wtaanni 12 aka samu rufewar ayyuka yah aura samar da sabbi.”

“Duba ga nazarinmu, alkaluma ne na gaskiya, Rufe kamfanoni 767 a Nijeriya bai kai kusa da rufe kananan kasuwanci 345 a Ingila a wannan lokacin ba.”

“Haka kuma ba za a iya kwatranta adadin da kamfanoni 460,000 da ake rufewa dub bayan watanni uku a China ba, ko kananan sana’o’I 10,655 da aka rufe a tsakanin 2022-2023 a India.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa a yanzu haka kamar yadda Hukumar NAFDAC ta bayyana, an amince da bukatar da aka nema ta gina kamfanonin samar da magunguna guda 104 a Nijeriya, kuma an kammala kaso 35 na ginin kamfanonin da aka amince da su din.

Kungiyar ta IMPI ta kuma ce akwai kungiyoyin nazari da auna tattalin arziki da dama da ke mantawa da habaka ko ingantuwar wasu kasashen duniya, inda suke mayar da hankali ga alkaluma marasa kyau.

"Habakar da Nijeriya ke yi na da nasaba da yadda kamfanonin da ke kasar ke da adadi 27 na jerin kamfanoni 100 mafiya karfi a Afirka.

Akwai kamfanonin Nijeriya biyu da ke sahun gaba a Afirka; Afex Commodities Exchange Ltd da Moniepoint Inc - Wannan ya sanya dole kasar ta yi murna duk da kalubalen da take fuskanta."

“May and Baker Nigeria kamfanin samar da magunguna ne a Nijeriya, an bayar da rahoton ya mayar da hankali wajen samar da sabbin kayayyaki bakwai, daga cikin kayayyaki 20 da za su kaddamar a 2024.”

Haka zalika akwai kamfanin Seplat ANOH Gas. Ana sa ran kamfanin zai rage yawna iskar carbon a kasar.

Tashar jiragen ruwa ta APM da ke Apapa ce mafi girma a Nijeriya. Shekaru 17 da suka gabata APM suka karbi tashar Apapa, kuma sun zuba jarin sama da dala miliyan $438 wajen inganta kayan aiki da ke wajen.

A watan Yunin 2023, tashar ta marabci jirgin dakon kaya mafi girma da ya zo Lagos jirgin Kota Contik na kasar Singapore.

“A irin wannan kasuwanci dai, masu zuba jari sun kasha dala biliyan $1.5 a tashar jiragen ruwa ta Lekki. Ita kadai ce tashar jiragen ruwa mafi zurfi a Nijeriya. Ana sa ran kara girman tashar ta yadda za ta iya daukar kwantenoni miliyan shida a lokaci guda.

Wani kamfani da ya sake bunkasa a Nijeriya shi ne na safarar jiragen sama; Air Peace, shi ne kamfanin jiragen sama mafi girma a Yammaci da Tsakiyar Afirka. A yanzu na sauya labara safarar jiragen sama a yankin.

Kamfanin AA Rano ya yi fice wajen sayar da albarkatun iskar gas. Kamfanin na da cibiyoyi kusan a dukkan fadin Nijeriya. Yana bayar da gudunmowa wajen habakar tattalin arzikin Nijeriya.

Tattalin arzikin Nijeriya na habaka sosai a karkashin shugabancin Bola Ahmad Tinubu, saboda irin manufofin gyara da habaka da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

TRT Afrika da abokan hulda