Matsakaicin farashin kilo daya na albasa ya ƙaru da kashi 122.9 Hoto/AP

Albasa da agada da dankalin Hausa na daga cikin kayan abincin da suka fi tsada a cikin shekara, a cewar Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya (NBS).

Jerin kayan abincin na cikin sabon rahoton da NBS ta fitar a makon nan, inda ya nuna kayan abincin sun yi tsananin tsada a watan Disamban 2023 idan aka kwatanta da farashinsu na watan Disamban 2022.

Matsakaicin farashin kilo daya na albasa ya ƙaru da kashi 122.9 zuwa naira 971.9 a Disamban 2023, yayin da a Disamban 2022 farashin nata bai wuce naira 435.

Ita kuwa agada farashinta ya karu ne da kashi 114.6, wato daga naira 347.7 zuwa naira 746.

Farashin dankalin Hausa ya ƙaru da kashi 105 cikin 100 duk kilo ɗaya daga kashi 85.8 cikin 100 a 2022.

TRT Afrika