Virginia Mabhiza za ta soma aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamba.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya nada Virginia Mabhiza a matsayin mace ta farko a mukamin babbar lauyar gwamnati ta kasar wato Atoni Janar.

Nadin Mabhiza zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamba, a cewar wata sanarwa da sakatariyar majalisar ministocin kasar ta fitar.

Sanarwar ta bayyana Mabhiza a matsayin gogaggiya a fannin shari'a kan laifuka da kuma kararraki da kare farar-hula.

Al'umma kasar, wacce ke kudancin Afirka, sun bayyana farin cikinsu game da wannan nadi da aka yi wa Mabhiza musamman la'akari da wani rahoto na 2021/2022 da aka fitar kan ci-gaban dan'adam da ya yi nuni kan yadda Zimbabwe ke baya a matakin bai wa mata mukamai da suka shafi shugabanci da siyasa.

Duk da cewa dokar Zimbabwe ta tanadi wakilcin mata da maza daidai gwargwado a kowane mataki, matsayin mata yana baya.

Kafin wannan nadi Mabhiza na rike da matsayin sakatariyar ma'aikatar shari’a da kuma harkokin majalisun kasar, mukamin da ta rike tun daga shekarar 2013.

A yanzu haka za ta maye gurbin Yarima Machaya wanda ke shirin yin ritaya.

Kazalika ta kasance sakatariyar harkokin tsarin mulkin kasar a gwamnatin tsohon Shugaba Robert Mugabe da ya raba madafun iko da 'yan adawa Morgan Tsvangirai.

TRT Afrika