Daga cikin waɗanda suka halarci taron na sarakunan gargajiya akwai Sarkin Musulmin Nijeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III da Ooni na Ife. Hoto: State House

Tun da aka fara batun shirya zanga-zanga a Nijeriya, a iya cewa wannan makon ya kasance wanda aka ga gwamnati tana ta kai kawo da ganawa da masu ruwa da tsaki a ƙasar, don yin “iya bakin ƙoƙarinta” na hana faruwar boren.

An shafe kusan mako uku ana ta kiraye-kiraye musamman a kafafen sada zumunta kan wata zanga-zanga da mafi yawa matasa ne suka goyon bayan a yi ta, “don nuna ɓacin rai a kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.”

Baya ga hukumomin tsaro kamar na ‘yan sanda da sojoji da hukumar DSS da suka dinga fitar da sanarwar gargaɗi da jan kunne, a ranar Alhamis Shugaba Bola Ahmed Tinubu sai da ya yi ganawa har uku da wasu ɓangarorin al’umma.

Ya fara ne da yin taro da gwamnonin jam’iyyarsa ta APC, wanda ya biyo bayan ganawarsa da ya yi da gwamnonin ƙasar 36 ne a ranar Laraba.

Taron na Tinubu da gwamnonin APC ya ɗauki tsawon awa ɗaya da minti 15, wanda ana kammala shi sai kuma ya shiga ganawa da sarakunan gargajiya daga faɗin ƙasar har tsawon awa ɗaya da rabi.

Da wajen misalin ƙarfe 4.30 na yamma agogon Nijeriya ne sai kuma Shugaban Ƙasar ya gana da malaman addinin Musulunci duka dai a Fadar Aso Rock Villa.

Batu ɗaya ne Tinubu ya tattauna da duka wadannan masu ruwa da tsaki, wato shi ne ƙoƙarin ganin cewa an hana gudanar da zanga-zangar da ake shirin shafe kwana 10 ana yi, wato daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta mai kamawa.

Taron sarakunan gargajiya

Daga cikin waɗanda suka halarci taron na sarakunan gargajiya akwai Sarkin Musulmin Nijeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III da Ooni na Ife da Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi da Sarkin Zazzau Ahmen Bamalli da sauran su.

A sanarwar bayan taro da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, an ambato Tinubu yana cewa ya damu da halin da ake ciki a ƙasar kuma yana aiki ba dare ba rana don ganin ya sauke alkawuran da ya ɗauka.

"Lallai ni ne na nemi kujerar nan har ma na nemi goyon bayan wasu daga cikinsu. Don haka ba ni da wani uzurin da zai hana ni yin aikin nan cikin gaskiya da himma," ya ce.

Wasu labaran masu alaƙa

Shugaba Tinubu ya buƙaci sarakunan da su gaya wa al'ummominsu sahihiyar niyyar gwamnati ta cika alkawarin gwamnatinsa na Sabunta Fata, wato Renewed Hope. “Yanzu, muna aika kudi ga kananan hukumomi. Na yi wa gwamnoni jawabi a yau kan wannan batu. Na yi ta rabon takin zamani da shinkafa, da sauran kayayyaki don tallafa wa ‘yan kasa su farfado.

"Ina tabbatar muku, ’yan Nijeriya, za a samu sauƙi nan ba da daɗewa ba. Ina mai tabbatar muku, za a farfado da tattalin arzikin nan, za a ci gaba da rayuwa, kuma za a samu ci gaba,’’ Shugaban ya jaddada.

A nasu jawabin na bayan taron, sarakunan sun nemi masu shirya zanga-zangar da su nemi tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, suna gargaɗin cewa akwai yiwuwar wasu ɓata-gari su shiga zanga-zangar su mayar da ita tashin hankali.

“To, saƙon da za mu kai wa al’ummominmu shi ne a kwantar da hankula, mu yi hakuri, sannan mu saurari maganganun hikima da ke fitowa daga bakin sarakunan gargajiya da na gwamnoni saboda mun yi magana da Shugaban Ƙasa kuma ya ba mu bayanai a kan shirye-shiryen da yake da su na tsawon lokaci,” in ji shi.

Malaman Musulunci

Shugaban Ƙasa ya fara ganawa da su da misalin ƙarfe 4.30 na yamma inda suka shafe awa ɗaya a rabi suna tattaunawa.

A wani bidiyo da TRT Afrika Hausa ta gani a gidan talabijin na TVC, an ga shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa Sheikh Bala Lau da sakatarensa Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Karibullah Nasiru Kabara.

Akwai kuma Malam Ibrahim ɗan Sheikh Dahiru Bauchi, da Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo da kuma Farfesa Mansur Sokoto.

Sai dai duk da yake shi ma wannan taron a kan batun zanga-zangar ne, ba mu samu wani ƙrin bayani kan yadda ya gudana ba.

TRT Afrika