Zanga-zanga ta barke a Kano kan hukuncin Kotun Daukaka Kara na zaben gwamna

Zanga-zanga ta barke a Kano kan hukuncin Kotun Daukaka Kara na zaben gwamna

Zanga-zanga ta ɓarke a Kano kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kwanan nan kan zaben gwamnan jihar.
Kotun daukaka kara ta kwace nasarar Abba K Yusuf ta tabbatar da Nasiru Gawuna.

Zanga-zanga ta ɓarke a Kano kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kwanan nan kan zaben gwamnan jihar.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun yi ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zangar a unguwar Dan Agundi da ke cikin birnin Kanon.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan bayyanar kwafi na hukuncin Kotun Daukaka Kara, wanda ake zargin ya saɓa wa hukuncin baki da ta sanar a makon da ya gabata, inda ta jaddada hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe na kwace nasarar Abba Kabir Yusuf na NNPP, ta bai wa Nasiru Gawuna na PDP.

A bidiyoyin da TRT Afrika ta gani a shafukan sada zumunta na zanga-zangar da aka yada, an ga mutane suna gudu a daidai titin Gidan Murtala, sakamakon harba hayaki mai sa hawaye da ƴan sanda ke yi.

Dama tun a wancan makon da Kotun Daukaka Karar ta yake hukuncin, rundunar 'yan sandan jihar ta sanar da matakan da ta dauka don hana barkewar rikici gabanin da bayan sanar da hukuncin kotun.

A sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce “Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel tare da sauran shugabannin hukumomin tsaro, sun tura isassun jami’ai da kayan aiki don gano wurare masu muhimmanci a jihar, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi tare da daƙile duk wani yunƙuri na tayar da hargitsi ko rashin bin doka da oda”.

A wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya rawaito, wani mutum da kafar ta yi hira da shi ya ce lamarin ya fara ne a lokacin da "da safiyar yau inda wasu 'yan jihar Kano suka taru a filin Mahaha don yin addu'o'i cikin lumana, cikin rashin sa'a bayan gabatar da addu'ar sai ga 'yan sanda sun far mana," ya ce.

A wasu bidiyoyin kuma an jiyo wasu na sowar cewa ”Abba muka zaba kuma shi muka dangwalawa kuri'unmu."

A makon da ya wuce ne Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta fara yi tun farko na soke zaben Abba Kabir Yusuf, a ranar 30 ga waran Satumban 2023.

Sai dai jim kadan bayan hakan, jam'iyyar NNPP ta sanar da cewa ba a ba ta kofin takardun hukuncin ba.

A ranar Talata kuma sai wasu takardu suka yadu, da ke nuna cewa daga kotun suke, inda suka zo da wani abu da ya ba da mamaki.

Sakin layi na karshe na shafi na 68 na hukuncin ya ce: "Zan kammala da cewa an ba da nasara kan wannan daukaka kara ga mutum na farko da aka kai karar sa ba wanda ya daukaka karar ba," kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Wannan batu kuma shi ne ya jawo rudani inda NNPP take ikirarin ita aka bai wa nasara kamar yadda ita ma APC take yi.

TRT Afrika da abokan hulda