Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya ce zai garzaya Kotun Kolin Nijeriya don neman hakkinsa bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da soke zabensa a matsayin gwamna.
Gwamna Abba Gida-Gida, kamar yadda aka fi saninsa, ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar ga al'ummar jihar ranar Juma'a da maraice.
Ya yi jawabin ne bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Kano cewa Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC ne halastaccen gwamnan jihar a zaben da aka gudanar a watan Maris na 2023.
A wancan hukuncin, kotun ta cire kuri'a 165,663 daga kuri'un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa kuri'un hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.
Labari mai alaka: Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da Gawuna a matsayin gwamnan Kano
Sai dai jim kadan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara a Kotun Daukaka Kara da ke Abuja yana kalubalantar hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben.
Amma a hukuncinta na ranar Juma'a, Kotun ta ce Abba Kabir Yusuf ba mamba ba ne na jam'iyyar NNPP a lokacin da aka gudanar da zaben 2023.
'Abin bakin ciki'
Sai dai a jawabinsa ga al'ummar Jihar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaici kan yadda Kotun ta kori karar da ya kai mata.
"Abin bakin ciki shi ne ita kanta wannan kotu ta gaba ta zauna ta kori karar da muka kawo...dalilinsu guda daya ne. Dalili shi ne jam'iyyar APC ta jihar Kano ta kai kara a kan zamana mamba na jam'iyyar NNPP," in ji shi.
Ya kara da cewa: "Wannan korar kara da aka yi a yau muna gani ba a yi mana adalci ba. Haka kuma ba a yi wa al'ummar jihar Kano adalci ba domin mu mun sani al'ummar Jihar Kano sun fito kwansu da kwarkwata sun kada mana kuri'u."
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce zai garzaya Kotun Koli domin ganin ta sauya hukuncin da kotunan baya suka yanke.
"Dangane ga wannan muka yi shawara da masu ruwa da tsaki a kan cewar lauyoyinmu su shigar da wata sabuwar kara a Kotun Koli ta Nijeriya. Muna da yakini idan Allah ya yarda, wannan kotu ta karshe za ta kwato wa al'ummar jihar Kano wannan hakki nasu, haka kuma za ta kwato mana mu ma hakkinmu kuma za ta kori wancan rashin adalci da aka yi mana baki daya," a cewar gwamnan na Kano.