A ranar Litinin Zambia ta sanya hannu kan yarjejeniya da China don kafa kamfanin samar da alluran riga-kafin cutar kwalara ta farko a kasar da ke kudancin Afirka.
Kashin farko na aikin zai lashe dala miliyan 37, inda ake sa ran samar da allurai miliyan uku ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Hukumar Bunkasa Masana'antu ta Zambia da Kamfanin Jijia Mai Samar da Magunduna na China.
Da yake bayani a yayin sanya hannu kan yarjejeniyar a Gidan Gwamnati da ke babban birnin Lusaka, Shugaban Kasar Zambia Hakainde Hichilema ya shaida cewa matakin wani bangare ne matakan yaki da cutar a fadin kasar, wanda zai kai ga kara amfanar jama'ar kasar.
"Muna kuma aike wa da sakon cewa Zambia, Afirka da duniya baki daya na iya aiki tare. Dole ne a kalli Zambia a matsayin cibiya, waje da za a iya samar da kaya don amfanin wasu kasashen.
"Idan kuka kalli yawan jama'ar Afirka, suna habaka da sauri," in ji Hichilema kamar yadda tashar talabijin din kasar ta rawaito.
Aiki mai saukin kashe kudade
Hichilema ya ce yana sa ran aikin ba zai ci kudade da yawa ba, kuma babu wata ƙumbiya-ƙumbiya wajen aiwatar da shi, aiki ne na kubutar da rayukan 'yan kasa.
Ya kara da cewa a yayin da ake gaf da samar da kayayyaki, China za ta samar da alluran riga-kafin cutar kwalara kimanin miliyan uku.
A wannan shekarar cutar kwalara ta bulla a Zambia inda sama da mutane 400 suka ras arayukansu, ta kuma kama sama da mutane 10,000, wanda hakan ya sanya mahukunta rufe makarantu a fadin kasar bayan karewar hutun karshen shekara.
Ana yawan samun bullar cutar kwalara a kasar da ke kudancin Afirka, musamman a lokacin damina, ana iya magance cutar, amma kuma tana yin ajalin rayuka.