Zaftarewar kasa da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya na sa’o’i sama da hudu ta kashe akalla mutum ashirin da uku a birnin Yaounde na kasar Kamaru.
Iftila’in da ya auku a unguwar Mbankolo ranar Lahadi ya rutsa da gidaje 25 kamar yadda gidan rediyon gwamnatin Kamaru ya ambato jami’ai yana cewa.
"Jiya mun samu gawar mutum 15 yayin da yau kuma gano gawar mutum takwas. Har yanzu muna ci gaba da neman karin gawarwaki," a cewar wani jami'in hukumar kwana-kwana David Petatoa Poufong a hira da menama labarai.
Rahotanni sun ce ruwa ya mamaye kan tituna, lamarin da ya hana ‘yan kwana-kwanan kai dauki ga mutanen da lamarin ya rutsa da su cikin sauki.
Rahotannin sun ce cikin dare ne lamarin ya auku, kuma mutanen gari ne suka fara kai wa mutanen da abin ya shafa dauki.
Ko a watan Nuwamban bara zaftarewar kasa ta kashe mutum 14 a babban birnin kasar ta Kamaru.
A ranar Lahadi an yi gargadin cewa za a yi ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar Nijeriya da ke makwabtaka da Kamaru sakamakon sakar ruwa daga wata madatsar ruwa a Kamaru.