Mutum takwas daga ciki har da yara biyu sun rasu bayan da wasu gidaje da aka gina kan wani wuri da aka cike da bola ya zaftare a ranar Asabar a Kampala babban birnin Uganda.
Kafafen watsa labarai na cikin gida sun bayyana cewa mutane da dabbobi sun rasu sakamakon zaftarewar ƙasar da ta faru a tsohuwar bolar da ke Kiteezi da ke arewacin Kampala bayan ruwan sama mai ƙarfi.
"Abin takaici mutum takwas zuwa yanzu sun rasu, manya shida da yara biyu," kamar yadda hukumar gudanarwa ta birnin Kampala KCCA ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X.
Hukumar ta KCCA, wadda ke da wurin jibge bola, ta bayyana cewa an ceto mutum 14 inda aka kai su asibiti. Sai dai ba ta bayyana halin da suke ciki ba.
Aikin ceto
"Har yanzu ana gudanar da aikin ceto kuma za mu ci gaba da bayar da bayanai da zarar sun shigo," kamar yadda ta ƙara da cewa.
Hotuna daga wurin da lamarin ya faru sun nuna yadda motar rushe gini ke aikin tono ɓaraguzai.
'Barazana ga lafiya'
"Jami'anmu tare da wasu hukumomin gwamnati na can suna ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da aminci a wurin da kuma kare faruwar irin hakan a gaba," kamar yadda ya ƙara da cewa.
Jaridar Daily Monitor, wadda jarida ce mai zaman kanta a Uganda a shafinta na intanet ta bayyana cewa shugaban KCCA Erias Lukwago tun a watan Janairu ya yi gargaɗi kan cewa mutanen da ke aiki sannan suke zaune a kusa da Kiteezi na cikin barazanar abubuwa da dama, ciki har da ambaliyar bolar.