Gundumomi 11,715 daga cikin 23,293 sun kammala ƙirga ƙuri'a, inda jam'iyyar ANC ke kan gaba a larduna bakwai, in ji kafar watsa labarai ta SABC. / Hoto: Reuters

Sama da kashi 50 na masu jefa ƙuri'a a Afirka ta Kudu a zaɓen 2024 ne suka fita rumfunan zabe, in ji kafar yaɗa labaran ƙasar.

Gundumomi 11,715 daga cikin 23,293 sun kammala ƙirga ƙuri'a, inda jam'iyyar ANC ke kan gaba a larduna bakwai, in ji kafar watsa labarai ta SABC.

Jam'iyyar Haɗin Kan Dimokuraɗiyya ta DA na kan gaba a Western Cape da kashi 52.4 na ƙuri'in da aka jefa.

Sabuwar jam'iyyar uMkhonto weSizwe na kan gaba a lardin KwaZulu-Natal da kashi 45.4.

Jam'iyya mai mulki ta ANC na kan gaba da kashi 35 na ƙuri'un da aka jefa a Gauteng da kuma kashi 72 a lardin Limpopo.

Kur'iun da aka soke

A yayin da ake ci gaba da kirga kuri'un, adadin kuri'un da aka soke na kara yawa.

A yayin da aka kammala ƙirge a kashi 48 na ƙuri'un lardunan, adadin ƙuri'un da aka soke ya haura 86,000.

Ana soke ƙuri'a ne idan ba a danna tawada da kyau ba a kan takardar zaɓe.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta gargaɗi 'yan ƙasa cewa duk wanda aka kama ya ɗauke akwatun zaɓe zai fuskanci hukunci a gaban kotu.

An fitar da gargaɗin ne bayan da a ranar zaɓe Hukumar Zaɓen ta nemi wasu takardun jefa ƙuri'a sama ko ƙasa ta rasa a makarantar Matamzana Dube da aka kafa rumfunan zaɓe.

Janaral Manaja na Hukumar Zaɓen Granville Abrahams ya bayyana cewa "Hukumar na rike ƙuri'u har tsawon watanni shida kafin ta zubar da su. Muna so mu gano waɗannan ƙuri'u da suka ɓata don ajiye su. An ɗauke su ne a cikin mota buɗaɗɗiya."

"A lokacin da muka isa wajen da muke tafiya, sai muka gano an ɗauke akwatin jefa ƙuri'a guda ɗaya. Ina so na tabbatar da cewa an ƙirga waɗannan ƙuri'u kuma za a yi aiki da su," in ji Abrahams.

TRT Afrika