Kotun sauraren kararrakin zaben Nijeriya da ke Abuja ta soma zaman yanke hukunci kan karar da manyan 'yan takarar shugabancin kasar a zaben 2023 suka shigar ta neman soke zaben da aka yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Alkali Haruna Tsammani ne yake yanke hukuncin bisa taimakon alkalai hudu - Mai Shari'a Stephen Adah, Mai Shari'a Monsurat Bolaji-Yusuf, Mai Shari'a Moses Ugo da kuma Mai Shari'a Abba Mohammed.
Manyan 'yan siyasa da jami'an jam'iyyun kasar ne suka hallara a kotun domin ganin yadda hukuncin zai kaya.
Wadanda ke halartar zaman kotu sun hada da mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje da wasu gwamnonin jihohi na jam'iyyar.
Kazakila gwamnan jihar Bauchi Bala Mohamed na jam'iyyar PDP na cikin wadanda suka je kotun.
Labarai mai alaka: 'Tinubu ba ya fargaba kan hukuncin da kotun zabe za ta yanke'
Ana watsa shari'ar kai-tsaye ta gidajen talabijin da sauran kafofin watsa labarai.
Tuni hukumomin tsaron Nijeriya suka karfafa tsaro a fadin kasar saboda fargabar barkewar tarzoma, suna masu shan alwashin dakile duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye.
A watan Fabrairu aka gudanar da zaben shugaban kasar kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara inda samu kuri'a 8,794,726 -- wato kashi 37 na kuri'un da aka kada.
INEC ta ce Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne yake biye masa da kuri'a 6,984,520 -- kashi 29, yayin da dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi ya samu kuri'a 6,101,533 -- kashi 25.
Sai dai Atiku Abubakar da Peter Obi sun garzaya kotu inda suke kalubalantar zaben.
Abubuwan da Atiku da Obi suke nema a wurin kotu
- Atiku ya bukaci kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ta sa INEC ta gudanar da sabon zabe wanda shi da Tinubu za su fafata.
- Ya ce idan ba haka ba, ya kamata kotu ta soke zaben gaba daya sannan a sake gudanar da shi.
- Atiku ya ce Tinubu bai samu yawan kuri'un da suka isa a ayyana shi a matsayin shugaban kasa ba kuma bai cacanci tsayawa takara ba lokacin da aka gudanar da zabe.
- Mr Peter Obi ya nemi kotun sauraren kararrakin zaben ta soke zaben sannan INEC ta gudanar da sabo kuma kada ta bari Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da jam'iyyar APC su shiga zaben.
- Kazalika dan takarar na LP yana so kotu ta bayyana cewa Tinubu bai lashe zaben da kuri'u mafi rinjaye ba.
- Obi ya bukaci kotu ta kwace takardar shaidar yin nasara a zabe da INEC ta bai wa Tinubu, sannan ta ba shi (Obi) sabuwar shaidar lashe zaben shugaban Nijeriya.
- Peter Obi ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben kuma ita kanta INEC ta ki yin biyayya ga dokarta inda ta sanar da sakamakon zabe kafin a gama sanya shi a na'urar tattara sakamako.
Martanin Shugaba Tinubu
A nasa bangaren, shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya gaya wa kotun cewa Peter Obi bai cancanci kalubalantar nasararsa a zaben shugaban kasar ba.
Ya ce ba a bi ka'ida ba wajen tsayar da Mr Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa na LP.
Ya kara da cewa Peter Obi ya sauya sheka daga PDP zuwa LP kasa da wata daya kafin gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar.
Kazalika ya ce Atiku ba shi da hujjar da za ta sa a soke zabensa, yana mai bukatar kotun ta yi watsi da kararsa.