Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa ta kama Yunusa-Ari, Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa da ke arewa maso Gabashin kasar.
Wata sanarwa da kakakin rundunar CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Talata ta ce an kama jami'in ne bayan hukumar zabe ta kasa, INEC, ta bukaci hakan "bisa zargin sanar da 'yar takarar jam'iyyar All Progressives Congress a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar."
"Jami'an 'yan sanda da ke kula da shirya zabe da sanya ido a Abuja sun kama Barista Ari ranar Talata 2 ga watan Mayun kuma yanzu haka yana tsare a hannun 'yan sanda," in ji sanarwar.
Ta kara da cewa ana yi wa Kwamishinan Zaben tambayoyi da "zummar gano dalilan da suka sanya shi aiwatar da abin da ake zarginsa da yi a zaben da aka kammala a Jihar Adamawa."
CSP Olumuyiwa Adejobi ya kara da cewa 'yan sanda suna yin tambayoyi ga sauran jami'ai da mutane da ake zargi da hannu a badakalar zaben jihar ta Adamawa.
A watan jiya ne INEC ta bukaci babban sufeton ‘yan sandan kasar da ya gudanar da bincike da kuma tuhumar Barista Hudu Yunusa-Ari.
Kazalika ta bukaci Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ja hankalin hukumar da ke da alhakin nada kwamishinonin zabe kan halin da Kwamishinan Zaben ya nuna domin daukar mataki.
Barista Yunusa-Ari ya ja hankalin 'yan Nijeriya ne bayan ya sanar da Sanata Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa tun kafin a kammala tattara sakamakon zaben.
Jim kadan da sanar da sakamakon zaben, 'yar takarar ta APC ta sanar da amincewa da sakamakon zaben.
Sai dai gwamnan Jihar Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ya yi takara a jam'iyyar PDP, da wasu 'yan kasar sun yi tir da matakin na Barista Yunusa-Ari.
Daga bisani INEC ta sanar da cigaba da tattara sakamakon zaben inda ta sanar da Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara.