A ranar Alhamis ne hukumar zaben kasar Chadi ta ayyana Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar. / Hoto: AFP  

Shugaban mulkin Sojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya lashe zaben shugaban kasar a zagayen farko da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu, ya yi jawanbinsa na farko a matsayin zababben shugaban kasa a tsarin dimokradiyya.

"Yanzu ni ne zababben shugaban kasar 'yan Chadi baki daya... nasarar tana kara fitowa fili ba tare da wani cikas ba," a cewar Shugaba Deby a yayin wani takaitaccen jawabi da ya yi ta gidan talabijin, yana mai alwashin cika ''alkawuransa.''

An fitar da sakamakon zaben na wucin gadi a hukumance ne a ranar Alhamis, wanda ya tsawaita wa iyalan Idriss Deby tsawon shekaru da dama a kan karagar mulki.

Zaben na ranar Litinin ya kawo karshen mulkin soji da aka kwashe ana yi na tsawon shekaru uku a kasar, wadda ta mayar da hankali wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin Hamadar Sahel na Afrika.

Murnar nasarar da harbe-harbe

Hukumar zaben kasar ANGE ta ce Deby ya samu kashi 61.03 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda ya doke Firaiminista Succes Masra, wanda ya samu kashi 18.53 cikin 100 kacal, sakamakon da majalisar tsarin mulkin kasar ta tabbatar.

Sojoji a unguwannin da ke N'Djamena inda babban Ofishin jam'iyyar Masra ke da zama sun yi ta harbe-harbe da bindigogi sama bayan da aka bayyana sakamakon zaben, domin murnar nasarar Deby da kuma hana masu zanga-zanga taruwa, a cewar rahoton kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

A kusa da Fadar Shugaban Ƙasar da ke tsakiyar birnin N'Djamena, magoya bayan Deby sun yi ta kururuwa suna rera wakoki da kuma danna ƙararrawar ababen hawa da harba bindigoginsu sama suna murna, kamar yadda 'yan jaridar AFP suka rawaito.

Daidaitacciyar ƙidaya

Magoya bayan Masra, mai shekaru 40 kana masanin tattalin arziki, sun yi ta rike kuri'unsu da ya yi daidai da na hukuma, kana a wani jawabin da ya wallafa a shafinsa na Facebook 'yan awanni kafin a fitar da sakamokon zaben, Masra ya ce ƙidayar tawagarsa ''ya tabbatar da nasarar zabensa a zagayen farko''.

Masra ya kuma ƙara da cewa tawagar Deby, wanda sojoji suka shelanta a matsayin shugaban rikon kwarya shekaru uku da suka gabata, nan ba da jimawa ba za su sanar da cewa shi ya lashe zaben tare da ''sace nasarar da jama'a suka samu.''

Masra, wanda tsohon madugun 'yan adawa ne da aka nada a matsayin firaiminista a watan Janairu, ya bukaci 'yan Chadi da su "haɗa kansu tare da tattaki cikin lumana don tabbatar da nasararmu."

Sanarwar ta ranar Alhamis ta matukar ba da mamaki, kasancewar ta zo ne kusan makonni biyu gabanin ranar 21 ga watan Mayu da aka tsara sanarwa.

Deby da Masra sun fafata da wasu 'yan takara takwas da ba a san su ba.

Kasar Chadi ta kasance babbar aminiyar Faransa, wadda gwamnatocin sojin kasashen Afirka da suka haɗa da Mali da Burkina Faso da kuma Nijar waɗanda ta yi wa mulkin mallaka suka fatattaki dakarunta.

AFP