Shugaban Nijar Abdourahmane Tiani ya sha alwashin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar./Hoto: Fadar Shugaban Nijar

Ministan Sufuri da Kayayyakin Aiki na Nijar Kanal-Manjo Salissou Mahaman Salissou, ya ce nan ba da jimawa ba za a kafa kamfanonin jiragen sama na Nijar da kuma na ƙasashen AES.

Kamfanin dillancin labaran Nijar, ANP, ya ce ministan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ba da bayanai game da ma’aikatarsa a birnin Yamai.

"Ƙasarmu na da faɗi sosai, kuma mun bai wa hukumar sufurin jiragen sama (ANAC) umarnin saussauta wasu dokoki domin taimakawa wajen samar da waɗannan kamfanonin. Saboda haka, ANAC ta fitar da sharuɗɗan samun damar wucewa ta sararin samaniya da sauri da kuma damar sauka a ƙasar," in ji ministan.

Ya kuma bayyana cewa an sauƙaƙa hanyoyin samun takardun shaidar ayyukan jiragen sama a ƙasar.

Kazalika kamfanin dillancin labaran Nijar ya ambato ministan yana cewa an riga an kafa kwamiti domin gaggauta bayar da takardun da ake buƙata wajen samar da waɗannan kamfanonin.

Ministan ya ce wannan aikin , "wani ɓangare ne daga cikin dabarun duniya na buɗe (ƙasar) domin ƙarfafa hanyoyin da suka haɗa Nijar da makwabtanta da kuma sauƙaƙa sufuri a cikin ƙasar."

"Maƙasudin wannan shi ne tallafa wa fannin noma da kiwo domin bai wa manoma damar sayar da kayayyakinsu cikin aminci," a cewar ministan.

Ministan sufurin ya ce, "yana da muhimmanci a samu ƙwararrun ma’aikata da kuma kayayyakin aiki wajen aiwatar da wannan aiki kuma mun yi sa’a saboda muna da wannan ƙarewar."

“Kafa kamfanin jiragen saman tarayyar AES na cikin abubuwan da muka saka a gaba,” in ji ministan yana mai ƙarawa da cewa “wannan aikin na ci gaba cikin sauri kuma insha Allahu na ba da jimawa ba za mu samu wani kamfani mai kalan AES wanda zai haɗa manyan biranenmu tare da wasu wurare ".

Layin dogo daga Nijeriya zuwa Maradi

Kamfanin ANP ya kuma ambato ministan yana cewa ƙasarsa za ta kafa wata tashar jiragen ruwa ta kan tudu da kuma layin dogo a Maradi da Agadez.

Ministan ya ce samar da waɗannan ababen more rayuwar dama ce ga ƙasar Nijar a fagen haɗin kai a yankin da kuma cin gashin kai.

Ya ce tattaunawa game da tashar jirgin ruwa ta kan tudu ta Dosso ta sa an rattaɓa hannu kan yarjejeniya tsakanin masu ruwa da tsaki ciki har da Nijar da Benin domin ayyana makomar tashar.

Ya kuma ce kafa wannan tashar jirgin ruwa ta tudun zai sa a fara wani ɓangare na babban layin dogo.

Bugu da ƙari, ya ce a wani ɓangare na gina layin dogon, aiki na tafiya kan wani layin dogo daga Nijeriya zuwa Maradi bisa sharruɗan da shugaban ƙasa ya bayar kuma an fara tattaunawa da ‘yan kasuwa domin su taka muhimmiyar rawa wajen kafa wannan tashar jiragen ruwa ta kan tudun

Ya ƙara da cewa gina tashar jiragen ruwa na tudu a Agadez yana da alaƙa da ƙarasa gina layin dogo daga Ingazam zuwa Agadez, lamarin da zai ƙarfafa kayayyakin sufuri a yankin.

TRT Afrika