Gwamnatin Senegal ta sanar cewa za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ranar 24 ga watan nan na Maris.
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba da maraice bayan taron Majalisar Ministoci ta ƙasar.
"Shugaban Jamhuriya ya shaida wa Majalisar Ministoci cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Lahadi, 24 ga watan Maris na shekarar 2024," a cewar sanarwar da Abdou Karim Fofana, mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya sanya wa hannu.
"Kazalika shugaban Jamhuriya ya sanar da Firaiminista da ministoci batun kafa sabuwar gwamnati."
Sall, wanda ya hau mulki a 2012 bayan ya lashe zaɓe, ya ɗage zaɓen da ya kamata a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata ne sakamakon abin da ya kira "taƙaddamar da ake yi game da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da kuma fargabar yiwuwar sake samun tashin hankalin da aka yi a shekarar 2021 da 2023."
Dubban ƴan ƙasar ne suka gudanar da jerin zanga-zangar adawa da ɗage zaɓen a matakin da ƴan hamayya suka bayyana a matsayin juyin mulki.
Mutum aƙalla uku ne suka mutu sakamakon zanga-zangar da aka yi musamman a Dakar, babban birnin ƙasar.
Sai dai daga bisani Kotun Tsarin Mulkin Senegal ta yi watsi da matakin da Shugaba Sall ya ɗauka na ɗage zaɓen tana mai bayyana shi a matsayin haramtacce.
Ƴan hamayya sun yi zargin cewa Sall ya ɗage zaɓen ne domin jam'iyyarsa, wadda ta tsayar da Firaiminista Amadou Ba a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, tana tsoron shan kaye.