Wata kotun soji a Saliyo ta yanke hukuncin ɗauri ga sojoji 24 waɗanda aka samu da laifin yunƙurin juyin mulki ga gwamnatin Julius Maada Bio a watan Nuwamba.
An karanto hukuncin ne a kotun a ranar Juma’a da yammaci inda alƙalin kotun ya yanke hukuncin da ya kama daga shekara 50 zuwa 120 ga waɗanda aka samu da laifin.
Suna daga cikin mutum 27 waɗanda aka yi wa shari’a kan yunƙurin juyin mulki a ranar 26 ga watan Nuwamba inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari barikin sojoji da gidan yari biyu da sauran wurare tare da sako fursunoni aƙalla 2,200 da kashe sama da mutum 20.
Hukuncin ya biyo bayan ɗaure wasu fararen hula 11 a watan Yuli, da ‘yan sanda da jami’an gidan yari saboda rawar da suka taka a rikicin.
Kwamitin masu taya alƙali yanke hukunci mai ɗauke da mutum bakwai sojoji ya samu akasarin sojojin da aka yi wa shari’a da laifi bayan alƙalan sun shafe sa’o’i suna ƙoƙarin tattaunawa.
Mutanen sun fuskanci tuhume-tuhume guda 88 da suka hada da kisan kai, taimakon abokan gaba da satar dukiyar jama'a da tayar da tarzoma.
Daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin akwai laftanar kanal wanda aka yanke wa hukuncin shekara 120 a gidan yari. Iyalan wadanda aka yanke wa hukuncin sun yi ta kuka a cikin kotun yayin da ake karanto hukuncin da aka yanke.
Yunkurin juyin mulkin ya biyo bayan zaben da shugaba Bio ya yi nasara da kyar don tabbatar da wa'adi na biyu.