Sabon yunkurin da aka yi na tabbatar da tsagaita wuta tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces RSF ya gaza, lamarin da ya sa cikin mazauna Khartoum ya duri ruwa sakamakon rashin abinci da magunguna a birnin.
Yarjejeniyar tsagaita wutar ta awa 24 — wadda kasashe da dama da ke son kwashe 'ya'yansu suka roki a kulla baya an kwashe kwanaki ana rikicin — ta gaza yin aiki ranar Laraba da karfe 6 na yamma a agogon kasar, duk da alkawarin da bangarorin biyu suka yi.
Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an cigaba da yin gumurzu har safiyar Alhamis.
Ma'aikatar Lafiyar Sudan ta ce an kashe kusan mutum 300 yayin da aka jikkata 2,600.
Rundunar sojin Sudan ta ce an kwashe sojojin saman Masar 177 zuwa kasarsu, kwanaki kadan bayan dakarun RSF sun sauke su a garin Merowe da ke arewacin kasar.
Daruruwan dakarun Sudan sun gudu Chadi
A gefe guda, ministan tsaron Chadi ya ce sojojin Sudan kusan 320 sun tsallaka zuwa kasarsa don guje wa yakin da ake yi a can.
"Sun iso kasarmu, mun kwance musu damara kuma muka tsare su" ranar Lahadi, a cewar Janar Daoud Yaya Brahim a taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba.
- Rikicin Sudan: Dubban mutane na tserewa daga Khartoum saboda luguden wuta
- Fafutukar neman mulkin da ta rikide zuwa mummunan yaki a Sudan
Ya ce sojojin suna jin tsoro kada dakarun RSF su kashe su.
"Halin da ake ciki a Sudan abin damuwa ne, kuma mun dauki dukkan matakan da suka dace a game da rikicin," in ji ministan.
'Sulhu alheri ne'
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewa kasarsa na tattaunawa da dukkan bangarorin da ke rikici da juna a Sudan.
Ya ce idan har aka tsagaita wuta za a bude sararin samaniyar kasar inda ‘yan Turkiyya za su samu damar dawowa gida.
Minista Cavusoglu ya yi wannan jawabi ne a wajen taron buda-baki a garin Antalya na Turkiyya.
Cavusoglu ya ce suna magana da Shugaban Kasar Sudan na rikon kwarya da kuma kwamandojin Dakarun RSF yana mai cewa akwai yiwuwar a tsagaita wuta ranar Alhamis.
Ya kara da cewa sulhu shi ne mafita a rikici kasar sakamakon cigaba da kashe mutane da ake yi.