Sudan ta Kudu ce za ta fi fuskantar wannan matsala sakamakon gagarumar ambaliyar ruwa da ta yi fama da ita, in ji sanarwar./Hoto: AFP

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya World Food Programme (WFP) ya yi gargadi cewa yara sama da miliyan daya da dubu dari shida ne ake sa rai za su fuskanci matsalar tamowa a 2024 kuma Sudan ta Kudu ce za ta fi fuskantar wannan matsala.

Da yake yin nuni da alkaluman da ta tattara daga tsarin bin diddigin samar da abinci na Integrated Food Security Phase Classification (IPC), WFP a ranar Litinin ya ce "ana sa rai yara miliyan 1.6 'yan kasa da shekara biyar za su yi fama da tamowa” a shekara mai zuwa.

"Yankunan da suka yi fama da ambaliyar ruwa su ne suka fi fuskantar matsalar tamowa sakamakon yaduwar cutukan da ke da alaka da ruwa da kuma cunkoso, da kuma karancin samar samun isasshen abinci da gudanar da rayuwa," in ji sanarwar da shirin ya fitar.

Shi ya sa ake sa rai yankunan Sudan ta Kudu da suka yi fama da ambaliyar ruwa su za su fi fuskantar "matsanancin karancin abinci da yunwa" a watanni shida na farkon 2024, a cewar WFP.

"Wannan shi ne hakikanin abin da ke faruwa a wuraren da ke fama da matsalolin sauyin yanayi," in ji Mary-Ellen McGroarty, Daraktar WFP a Sudan ta Kudu. "Muna ganin yadda matsalar tasowa ke faruwa sakamakon yin rayuwa a wuraren masu cunkoson jama'a da kuma fama da cutukan da ake dauka sakamakon ambaliyar ruwa."

AA