Bazoum ya kasance ministan harkokin cikin gida kuma makusancin Issoufou, wanda ya sauka daga mulki bayan ya yi wa'adi biyu. / Hoto: AFP

Ƴar hamɓararren shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ranar Juma'a ta zargi tsohon shugaban ƙasar Mahamadou Issoufou da "hannu" a juyin mulkin da aka yi wa mahafinta watanni tara da suka gabata.

Sojojin Nijar sun tsare Bazoum da matarsa a fadar shugaban ƙasar da ke Yamai tun da suka yi masa juyin mulki ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

An yi wa Bazoum juyin mulki ne shekaru biyu bayan ya maye gurbin Mahamadou Issoufou a zaɓen da aka gudanar a Nijar, wanda ya kasance karon farko da wata gwamnatin dimokuraɗiyya ta miƙa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnati tun da ƙasar ta samu ƴancin kai.

"Abu mafi muni da zai yi wahala a fahimta shi ne yadda aka gano cewa Mahamadou Issoufou ne ya kitsa komai domin biyan buƙatu na ƙashin kansa," kamar yadda ƴar Bazoum wato Hinda Bazoum ta rubuta a wata maƙala da jaridar L'Autre Republicain ta wallafa.

Ta yi iƙirarin cewa, "juyin mulkin zai ba shi damar komawa kan mulki idan sojoji suka kwashe lokaci maras tsawo suna mulki sannan aka rubuta sabon tsarin mulki".

Jagoran sojojin da suka yi juyin mulkin Janar Abdourahamane Tiani babban na hannun-daman tsohon shugaban ƙasa Issoufou ne.

Shi ma Bazoum ya kasance ministan harkokin cikin gida kuma makusancin Issoufou, wanda ya sauka daga mulki bayan ya yi wa'adi biyu.

"Abin da yake matuƙar ɓata mana rai shi ne sanin cewa mutanen da muke da alaƙa ta kurkusa su ne suka ci amanarmu," in ji ƴar Bazoum.

"Shi (tsohon shugaban ƙasa) da mahaifina suna da dangantaka mai ƙarfi ta shekaru 33 kuma tare muka gansu... shi abokin mahaifina ne kuma ɗan'uwansa amma ya ci amanarsa ta hanyar yaudara."

A watan Yuli, Issoufou ya wallafa saƙo a soshiyal midiya da ke cewa a shirye yake ya tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki domin maido da Bazoum kan mulki.

Hinda Bazoum ta yi zargin cewa "sabuwar yaudarar" da Issoufou zai yi nan gaba ita ce, zai shigar da ƙara a sabuwar kotu domin a cire wa Bazoum rigar-kariya ta yadda kotun soji za ta zartar masa da hukunci, inda hakan zai sa Issoufou ya kasance "mutum ɗaya tilo" da jam'iyyarsu za ta tsayar takara idan sojoji suka yarda su miƙa mulki.

Ta ce ita da ƴan'uwanta "rayuwarmu ta kasance ba ta da wani muhimmanci tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli".

"A haƙiƙanin gaskiya, ni da ƴan'uwana mata muna cike da baƙin ciki domin kuwa ba mu yi magana da iyayenmu ba tun ranar 18 ga watan Oktoban 2023."

Ta yi kira ga "ƴan kasar da kuma ƙasashen duniya su sa baki domin kawo ƙarshen wannan mugunta da ake yi wa iyayenmu".

AFP