Mali

‘Yan tawayen Tuareg a Mali sun ce sun kashe sojojin kasar da dama a wani hari da suka kai a tsakiyar kasar.

A ranar Lahadi ‘yan tawayen sun bayyana cewa sun sake kwace wani sansanin soji bayan musayar wuta da sojojin a arewacin kasar.

A ranar Asabar sojojin sun sanar da cewa sun kirga gawarwakin soji 98 sai dai daga baya sun mayar da adadin 81.

Wannan ikirarin na zuwa ne a wata sanarwa daga kungiyar Azawad Movements wadda ke kawance da kungiyoyin ‘yan aware na Tuareg wadanda suke son mulkin Mali ta fitar.

Haka kuma ‘yan tawayen sun ce sun raunata gomman sojoji tare da kama biyar daga cikinsu a matsayin fursunoni, inda suka ce mayakansu bakwai sun mutu.

Lamari ne mai wahala a iya tantance gaskiyar ikirarin da ‘yan tawayen suka yi sakamakon wuraren lamuran suka faru sun yi nesa da gari.

Sansanin sojin da ‘yan tawayen suka kwace shi ne na hudu a jerin hare-haren da suke kaiwa tun daga watan Agusta, bayan tafiyar sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka shafe shekaru suna taimaka wa sojojin kasar.

Mohamed ElMaouloud Ramadane, wani mai magana da yawun CMA ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Lahadi cewa sun kwace iko da sansanin sojin Bamba da ke yankin Gao.

Sojojin Mali dai na fuskantar zafafan hare-hare daga kungiyoyin ‘yan tawayen wadanda ke da alaka da al Qaeda da IS.

‘Yan tawayen Tuareg sun shafe tsawon lokaci suna korafi kan cewa gwamnati ta yi watsi da su tare da neman iko da wani yanki na Sahara da ake kira Azawad.

Reuters