‘Yan ta’adda sun sace sama da mutum 80 a ƙauyen ‘Yar-Malamai da ke Ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne ƙasa da awa 24 bayan maharan sun kashe wasu sojoji a wani sansanin soji da ke yankin.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar wa TRT Afrika da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba shi da cikakken bayani kan yadda harin ya kasance.
Sai dai wani mazaunin yankin wanda ba ya so a ambaci sunansa ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa tun daga ranar Asabar ‘yan bindigan suka addabi yankin da hare-hare har zuwa ranar Litinin .
Ya bayyana cewa a ƙauyen na ‘Yar-Malamai, ‘yan bindigan sun sace mutum 80, amma a yau Laraba, ‘yan bindigan sun sako mutum 22.
Ya ƙara da cewa maharan sun kashe aƙalla mutum takwas waɗanda suka haɗa da sojoji huɗu da ɗan bijianti ɗaya sai farar hula uku.
“Sun ƙona gidana, sun ƙona ɗakunan matana da na iyayena, sun ƙona abincinmu, sun ƙona motata, akwai inji na huɗa wanda na siya 600,00 shi ma sun tafi da shi,” in ji shi.
“Ina tabbatar maka da cewa gidan da ya tsira a garin ‘Yar-Malamai bai wuce gida ɗaya ba domin har shaguna sun ƙone su.”
Ya bayyana cewa tuni mutanen garin suka watse inda wasu ke kan duwatsu a ƙauyukan makwabta domin samun mafaka.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin Nijeriya da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Gwamnatin ta Katsina a kwanakin baya ta kafa wata rundunar tsaro ta ‘yan bijilanti domin daƙile matsalolin masu garkuwa da mutane, sai dai duk da wannan runduna, hakan bai sa ‘yan bindigan sun fasa kai hare-hare ba.