Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana buƙatar gaggawa wajen haɗa kai don yaƙi da ta’addanci da sauran matsaloli na rashin tsaro a Yammacin Afirka.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Tuggar ya ce daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2024, an samu hare-haren ‘yan ta’adda 800 a Yammacin Afirka, musamman a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.
Ya ƙara da cewa sama da mutane 7,000 ne suka mutu sakamakon hare-haren na ta’addanci a yankin.
“Dole ne mu haɗa kai waje guda don magance matsalolin tsaro, kuma mu yi aiki ba gajiyawa domin tabbatar da tsaro, dimokuraɗiyya da cigaban yankinmu,” in ji Tuggar.
Ya ƙara da cewar a yayin taron, sun kuma sake nazari da duba kan Tsarin Dimokuraɗiyya da Shugabanci na ECOWAS, inda ya kuma yaba da ayyukan samar da zaman lafiya da taimakon jinƙai da ake bayarwa a yankin.
Ƙasashen Yammacin Afirka dai suna fama da hare-hare na ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ISIS da Boko Haram ko ISWAP.