An sauya inifam din 'yan sanda sau da dama tun bayan samun 'yancin kai. Hoto/Reuters

Aƙalla mutum 121 ‘yan sandan Nijeriya suka kama a jihohin Benue da Filato waɗanda ake zargi ‘yan ƙungiyar asiri ne.

An kama su ne a lokacin da suka yi wani gangami na ƙungiyar mai taken 7/7.

Tun a makon da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan Nijeriyar ta yi gargaɗi dangane da gangamin da ƙungiyar The Neo Black Movement ke shirin yi.

A sanarwar da ta fitar, rundunar ‘yan sandan Jihar Filato a ranar Litinin ta ce ta kama mutum 118 a ranar 7 ga watan Yuli, a ranar da suka yi gangamin murna da kuma shigar da sabbin mutane cikin ƙungiyar.

Ya kara da cewa sahihan bayanan sirri da hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro ne suka kai ga kama mutanen a wurare daban-daban a jihar.

Ya bayyana cewa tun daga ranar, ‘yan ƙungiyar asirin ba su ƙara yin wani taro a ko ina a jihar ba shi ya sa ma ba a sake samun labarinsu a jihar ba.

Adesina ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotun da zarar an kammala bincike.

A Jihar Benue kuwa, rahotanni sun ce matasan sun fito gangamin ne a garin Gboko a ranar 7 ga watan Yuli.

Sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Catherine Anene ta ce an kama mutum uku da ake zargi.

TRT Afrika