'Yan sandan sun ce mutanen sun ƙunshi 'yan Nijar da kuma waɗanda baƙi ne da suka shiga ƙasar. / Hoto: RTN

‘Yan sanda a Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar kama wasu mutum goma kan zarginsu da satar babura da fashi da makami.

‘Yan sandan sun kama mutanen ne a Matameye inda rahotanni suka ce mutanen sun fito daga gungu daban-daban duka waɗanda suka shahara wurin aikata laifuka.

Bayan samun labaran yawaitar satar babura a birnin Matameye da ke yankin Zinder, sai kwamishinan ‘yan sandan yankin Kantche, Boubacar Altine, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin wanda hakan ya kai ga kama mutanen, kamar yadda jaridar ActuNiger ta ƙasar ta ruwaito.

Kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana, gungun na farko ya ƙunshi mutum mutum bakwai inda shida daga cikinsu ‘yan Nijar ne ɗaya kuma ba ɗan ƙasa ban inda dukkansu sun shahara wurin satar babura.

Gungu na biyu kuma ya ƙunshi mutum uku waɗanda biyu baƙi ne ɗaya kuma ɗan Nijar inda suka shahara wurin fashi da makami a kasuwanni inda suka fi mayar da hankali wurin satar wayoyi da kuɗi.

A lokacin da aka yi holen masu laifin, gwamnan yankin Zinder Kanal Issoufou Labo ya jinjina wa ayyukan jami’in tsaro tare da yaba wa kwamishinan ‘yan sanda Boubacar Altine da rundunarsa.

TRT Afrika da abokan hulda