Wata tawagar 'yan sandan Kenya 400 ta tashi daga birnin Nairobi ranar Talatar nan zuwa ƙasar Haiti don aikin wanzar da tsaro.
'Yan sandan, waɗanda za su jagoranci jami'an tsaro kimanin 1,000 na Majalisar Ɗinkin Duniya, za su fafata da gungu-gungu na masu aikata laifuka a Haiti domin maido da zaman lafiya a ƙasar.
"Muna alfaharin ganin tashin rukunin farko na 'Yan Sandan Ƙasarmu waɗanda za su kasance a tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya don aikin waznar da tsaro a Haiti," a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya Kithure Kindiki, a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ƙara da cewa manyan jami'an 'yan sanda na ƙasar Kenya da kuma jami'ai daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ne suka halarci bikin tashin 'yan sandan zuwa ƙasar da ke yankin Caribbea.
Tawagar ta ƙunshi zaratan 'yan sanda na rundunoni na musamman na Kenya waɗanda suka haɗa da Sashen Kai Ɗaukin Gaggawa da Sashen Gudanarwa da kuma 'yan sandan gama-gari.
A yayin da yake jawabi gabanin tura 'yan sandan a Kwalejin Horas da 'yan sanda da ke Embakasi, Shugaban Kenya William Ruto ya ce, "Kenya tana da tarihin jajircewa a aikin wanzar da zaman lafiya da magance rikici a duniya. Zuwan 'yan sandanmu Haiti zai kawo sauƙi ga rayuwar maza da mata da yara da suka tagayyara sakamakon rikicin 'yan bindiga."
Ya ƙara da cewa, "Za mu yi aiki da ƙasashen duniya domin maido da zaman lafiya mai ɗorewa a Haiti."
Haiti ta kwashe shekaru da dama tana fama da rikicin 'yan bindiga. Lamarin ya yi ƙamari a watanni baya bayan nan, inda 'yan bindiga suka riƙa sace mutane da kashe su da aikata migayun ayyuka.