Rundunar 'yan sandan Ghana ta kama masu zanga-zanga 49 a gaban fadar shugaban kasar (Jubilee House) da ke birnin Accra a ranar Alhamis, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
'Yan sandan sun ce sun kama masu zanga-zangar ne saboda yadda wadanda suka shirya ta wato kungiyar Democracy Hub ta yi "biris da hukuncin kotu wanda ya hana ta yin zanga-zanga a kusa da kuma kewayen fadar shugaban kasa daga ranar 21 zuwa 23 ga watan Satumban 2023," a cewar sanarwar.
Kungiyar ta shirya zanga-zanga ne don matsa wa gwamnatin kasar Ghana lamba kan yadda take tafiyar da tattalin arzikin kasar da kuma halin matsin rayuwa da al'ummar kasar ke ciki.
Masu zanga-zangar sun ce wasu mutane da suka zo kallon zanga-zangar sanye da bakaken da jajayen kaya – launuka da ake alakantawa da masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da tsadar rayuwa – su ma an kama su.
A nata bangaren rundunar 'yan sandan kasar, ta ce ba ta hana mutane 'yancinsu na yin zanga-zangar ba, idan har suna da tarihin yin zanga-zangar lumana a baya.
Rundunar ta ce abin da ya sa ba za ta amince da yin zanga-zangar a gaban fadar shugaban kasa ba shi ne "saboda waje ne mai cikakken tsaro da muhimmanci," a cewar sanarwar.
Gwamnatin Shugaba Nana Akufo-Addo tana ikirarin cewa matsalar tattalin arzikin da kasar take ciki tasirin annobar korana da yakin Rasha da Ukraine ne, wanda kuma ya haifar da tashin farashin kayayyaki a kasashen duniya da dama.