'Yan sandan sun ce akwai bukatar jama'a su zama suna da masaniya kan abubuwan domin tabbatar da tsaron kowa a jihar. Hoto/Reuters

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Bauchi ta gargadi jama’a kan wasu abubuwa wadanda take ganin za su iya kasancewa barazana ga al’ummar jihar musamman a watanni hudu na karshen shekara.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar inda ta ce akwai wasu bayanai da ta tattara inda ta gano akwai wasu nau’in barazana daban-daban da ake fuskanta a watannin karshen shekara da kuma bukatar daukar mataki kansu.

Haka kuma rundunar ta ce akwai bukatar jama’a su zama suna da masaniya kan abubuwan domin tabbatar da tsaron kowa a jihar.

Rikicin manoma da makiyaya

A daidai wannan lokaci da ake girbin amfanin gona ana yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Domin guje wa afkuwar wannan rikici, ‘yan sandan jihar sun yi kira ga manoman da makiyaya kan su guji aikata duk wani abu da zai iya jawo karya doka da oda.

“Sai dai ana shawartar manoma da su kwashe amfanin gonarsu cikin lokaci kafin makiyaya su soma kiwo inda lamarin zai iya jawo abin da aka ambata. Haka kuma ana gargadin duka makiyaya da su guji shiga gonaki kafin manoma su kwashe amfanin gonarsu.," in ji sanarwar.

Fashi da makami

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa fashi da makami na daga cikin laifukan da aka fi aikatawa a watanni hudu na karshen shekara.

“Don haka, binciken da ‘yan sanda suka yi kan laifuka na shawartar matafiya da su guji tafiyar dare da kuma tafiyar sassafe,” in ji sanarwar.

‘Yan sandan sun shawarci jama’a kan cewa a duk lokacin da suka yi dare, su nemi wurin da ya dace domin barci a nan, sai su ci gaba da tafiya idan safiya ta yi.

Garkuwa da mutane

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Bauchi ta ce ta gano cewa a shekarar 2022, matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta fi ta’azzara a watanni hudu na karshen shekarar.

Rundunar ta ce a shekarar 2023, ta fito da tsare-tsare kan yadda za a shawo kan matsalar garkuwa da mutane ta hanyar amfani da dabaru irin na zamani.

Jihar Bauchi dai na daga cikin jihohin da suka yi fama da garkuwa da mutane a kwanakin baya sai dai lamarin ya lafa.

Guje-guje da ababen hawa da tafiyar dare

Rundunar ‘yan sandan ta ce an samu matukar karuwar hadura kan hanyoyi sakamakon tafiyar dare da gudun da ya wuce kima.

Rundunar ta bukaci jama’a da su guji guje-guje da ababen hawa musamman lokutan da babu motoci sosai a hanya.

‘Yan sandan sun ce yin hakan zai rage afkuwar haduran kan hanyoyi wanda hakan zai rage asarar rayuka da dukiyoyi.

Satar amfanin gona

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa a irin wannan lokacin ne ake yawan satar amfanin gona. “Ana shawaratar manoma da su san gonakinsu da kyau da kuma gonakin makwaftansu ko kuma masu gonaki da ke kusa da su,” in ji ‘yan sandan.

Rundunar ta kara jaddada cewa manoma su sa ido kan amfanin gonarsu da kuma girbe su idan sun nuna domin guje wa sata, ko kuma afkawar dabbobi ko gobarar dare.

‘Yan-Sara-Suka

Rundunar ta bayyana cewa a irin wadannan watanni hudu na karshen shekara, sana samun matasa wadanda ke daba.

‘Yan sandan sun shawarci jama’a kan ko da yaushe su zama a ankare da kayayyakinsu.

Haka kuma ‘yan sandan sun bukaci jama’a kan su rinka ba matasan da ke tare da su shawarwari kan barin duk wasu halaye marasa kyau wadanda za su iya jawo rashin zaman lafiya a cikin al’umma.

TRT Afrika