Rundunar 'yan sandan ta ce tana gudanar da bincike kuma nan gaba za ta gurfanar da wadanda take zargin a gaban kotu. Hoto/Reuters / Photo: AA

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Borno ta tabbatar da kama wani mutum bisa zargin kashe matarsa a Maiduguri.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan an kashe wata matar aure a Bayan Gidan Dambe da ke Maiduguri.

Matar auren ‘ya ce ga dan majalisar Jihar Borno mai wakiltar Karamar Hukumar Ngala.

A wata sanarwa da rundunar ta aika wa TRT Afrika, ta ce ta kama mijin marigayiyar mai suna Adamu Alhaji Ibrahim mai shekara 31 da kuma wani Bukar Wadiya mai shekara 24.

“A ranar 18 ga watan Oktoban 2023 da misalin shida na yamma, wani Adamu Alhaji Ibrahim mai shekara 31 da ke Dikechiri Bayan Gidan Dambe a Maiduguri ya je ofishin ‘yan sanda na Gwange tare da wani Bukar Wadiya mai shekara 39 da wata mota mai lamba MAG 230 AP da lambar Chasis ANR742256679821 dauke da wata wadda Adamu Alhaji Ibrahim ya ce matarsa ce inda yake neman agajin ‘yan sanda.

“Daga baya sai aka tabbatar da da cewa matar sunanta Fatima Alhaji Bukar. Mijin ya bayyana cewa shi ma’aikacin Bankin UBA ne inda ya dawo gida da misalin biyar na yamma ya same ta kwance cikin jini,” in ji sanarwar.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa binciken wucin gadi da aka yi ya nuna cewa kafin kisan, ma’auratan sun samu rashin jituwa ne sakamakon zargin da ake yi wa mijin kan cewa yana hulda da wasu mata a gidansa na aure.

‘Yan sandan sun bayyana cewa bayan binciken da suka gudanar a cikin gidan, sun gano wata guntuwar tabarya da igiya da wani kafet wanda aka bata shi da jini da wuka da mota kirar Honda da kuma wani matashin-kai wanda aka bata da majina.

Haka kuma ‘yan sandan sun ce babu wasu alamu da ke nuna cewa an fasa gida an shiga, sakamakon mijin ne kadai yake da mukullin da zai iya bude gidan daga waje.

TRT Afrika