Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a Nijeriya ta ce ta yi nasarar kama mutane da dama da ake zarginsu da aikata laifuka da a ranar farko ta zanga-zangar ‘adawa da rashin shugabanci nagari’ da aka fara ranar Alhamis a faɗin ƙasar.
Zanga-zangar dai ta ranar farko ta rikiɗe ta zama rikici a sassan ƙasar daban-daban, lamarin da ya jawo sai da ‘yan sanda suka yi amfani da ƙarfi a wasu wuraren don shawo kan lamarin.
Sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Alhamis din mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a SP Abdullahi Kiyawa ta ce ta kama “mutum 269 da hannu a ɓarnata kadarorin al’umma da na gwamnati da sace-sace da tayar da tarzoma a ƙarƙashin fakewa da zanga-zanga da kuma cutar da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”
Cikin kayayyakin da ‘yan sanda suka yi nasarar ƙwatowa har da jarkokin man gyaɗa masu lita 25 da yawa da kayayyakin ofis da kayan abinci da sauran kaya masu daraja, in ji rundunar.
“A yanzu haka waɗanda aka kaman suna sashen binciken masu aikata laifuka na rundunar, kuma daga can za a kai su kotu bayan kammala bincike. Ana kuma ci gaba da kama mutane da ƙwato kayayyaki,” a cewar sanarwar wadda ta fito daga hannun Kwamishinan ‘Yan sanda na Kano, Salma Dogo.
Kwamishina Dogo ya jaddada aniyar rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, “don haka duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da rikici ko yin ɓarna ko satar dukiyar al’umma da ta gwamnati ko yada labaran ƙarya don ta’zzara yanayin da ake ciki, to kuwa zai fuskanci hukunci bisa tanadin shari’a.”
Kazalika ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi biyayya ga dokar taƙaita zirga-zirga ta awa 24 da aka sa a jihar, wadda ya ce ba za a lamunci karya ta ba.