Kayode Egbetokun ya ce rundunar ta zayyana tsare-tsare na kirkire-kirkire da za ta yi yayin da ake shirin tunkarar kalubalen shekarar 2025.

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kama mutum 30,313, tare da kwato bindigogi 1,984, da harsasai 23,250 a shekarar 2024.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta bayyana cewa Sufeto-Janar Egbtokun ya bayyana hakan ne a wani muhimmin taro da aka gudanar a ranar Talata, tare da manyan jami’an ‘yan sanda.

A cewarsa, taron wanda ya gudana a hedkwatar rundunar a Abuja, ya kasance dandalin nazarin nasarorin da rundunar ta samu a shekarar 2024.

Ya kara da cewa taron ya kuma zayyana tsare-tsare na kirkire-kirkire rundunar yayin da ake shirin tunkarar kalubalen shekarar 2025.

A nasa jawabin, Sufeto-Janar ya amince da kwazon aiki da jami’an ‘yan sandan suka nuna a tsawon wannan shekara, musamman irin gagarumin nasarorin da aka samu wajen rage aikata laifuka da kuma cudanya da al’umma, musamman ma ya nuna muhimmancin hada kai wajen samar da aminci tsakanin ‘yan sanda da jama’a.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A shekarar da ake nazari a kai, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta samu gagarumar nasara wajen magance miyagun laifuka, wanda ya kai ga kama mutum 30,313 da ake zargi da aikata munanan laifuka, da ƙwato bindigogi iri-iri har 1,984 da harsasai 23,250 daban-daban da kuma ceto mutum 1,581 da aka yi garkuwa da su.”

Adejobi ya kara da cewa rundunar ta shirya rungumar tsarin tunani na gaba a shekarar 2025, wajen mai da hankali kan kirkire-kirkire da ci gaban fasaha don karfafa dabarun gudanar da ayyukanta.

Ya kuma bayyana cewa rundunar tana da burin koyo daga abubuwan da suka faru a baya da kuma daidaita kalubalen da ke tasowa, da tabbatar da ingantaccen tsarin ɗaukar matakan kariya da kuma yin bincike.

“Rundunar za ta ba da fifiko kan kirkire-kirkire a fasaha da dabarun aiki a cikin 2025 da koyo daga gogewa yayin da muke samun ci gaba.

Sufeto-Janar din ya kuma karfafa wa manyan jami’ai gwiwa da su rungumi kayan aiki na zamani da ayyukan ci gaba da ke kara habaka tasirin rundunar wajen dakile laifuka da bincike.

“Yayin da al’ummar kasar nan ke shiga lokacin bukukuwan karshen shekara, rundunar ‘yan sandan Nijeriya karkashin jagorancin IGP Egbetokun, ta shirya tsaf don aiwatar da matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga daukacin ‘yan kasa.

“Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya nanata kudurin rundunar na karfafa hadin gwiwa da jama’a, da tabbatar da tsaro, da kuma bunkasa al’adar yin komai ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba,” in ji sanarwar.

TRT Afrika