An samu arangamar ne a unguwar Wuse da ke Abuja babban birnin Nijeriya a ranar Lahadi. / Hoto: NPF

Jami’an ‘yan sanda a Abuja babban birnin Nijeriya sun yi arangama da mabiya aƙidar Shi’a a ƙasar a daidai lokacin da ‘yan Shi’an ke gudanar da tattaki, lamarin da ya jawo asarar rayuka.

An samu arangamar ne a unguwar Wuse da ke babban birnin a ranar Lahadi.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Nijeriyar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa aƙalla jami’anta biyu sun rasu sannan uku sun jikkata sakamakon harin da ‘yan Shi’ar suka kai musu.

Sai dai wasu daga cikin mabiya aƙidar ta shi’a a shafin X sun wallafa bidiyo inda suke zargin ‘yan sandan da kashe musu mabiya da dama.

“Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja na son tabbatar da wani harin ba-zata da haramtacciyar Kungiyar Harka Islamiyya ta Nijeriya, wadda aka fi sani da ‘Yan Shi’a, ta kai wa wasu jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya da ke aiki a ofishin babban birnin tarayya Abuja da ke Wuse Junction kusa da turken bayar da hannu,” in ji sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda ta Abuja SP Josephine Adeh ta fitar.

“An kashe jami’an ‘yan sanda, uku ba su san inda kansu yake ba a asibiti, sannan motocin ‘yan sanda uku da ke sintiri an su kone kurmus,” in ji ta.

Sanarwar ta ce ‘yan Shi’an sun kai hari kan ‘yan sandan da adduna da ababen fashewa da wuƙaƙe.

TRT Afrika