'Yan sanda a Nijeriya sun fara gurfanar da wadanda aka kama yayin zanga-zanga a gaban kotu

'Yan sanda a Nijeriya sun fara gurfanar da wadanda aka kama yayin zanga-zanga a gaban kotu

An kama masu zanga-zanga da dama a jihohin arewacin Nijeriya kan zargin lalata dukiyoyin gwamnati da ta jama'a.
Wasu daga masu zanga-zanga da aka kama a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya. Hoto TRT Afirka

Ofisoshin 'yan sanda da dama a jihohin arewacin Nijeriya sun fara gurfanar da masu zanga-zangar da aka kama a yayin zanga-zangar adawa da mummunan shugabanci da aka yi a fadin kasar.

A yayin da ba a samu tashin hankali a yayin zanga-zangar a kudancin Nijeriya ba, a arewacin kasar ta rikide zuwa rikici inda aka samu asarar rayuka da dama, kadarori na biliyoyin naira, wanda hakan ya sanya aka saka dokar hana fita a jihohi biyar.

An kashe mutum 17

An samu rahotanni cewar akalla mutane 17 ne aka kashe a yayin zanga-zangar a babban birnin Abuja da jihohin Kano, Nigeri, Borno, Kaduna da Jigawa, inda aka kuma jikkata wasu da dama a ranar farko ta gudanar da zanga-zangar.

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Amnesty International ta soki yadda aka rinƙa amfani da karfin da ka iya kisa wajen magance masu zanga-zangar.

Kungiyar ta zargi 'yan sandan Nijeriya da kashe masu zanga-zanga 21 a fadin kasar.

Ana tuhumar masu zanga-zanga 1,135

'Yan sanda sun kama masu zanga-zanga da suka daga tutar Rasha a Kano, Kaduna, Gombe, Katsina, Yobe, Bauchi, Borno da Jigawa, inda aka bayyana za a gurfanar da su a gaban kotu.

Rundunar 'yan sanda a jihar Yobe ta bayyana za ta gurfanar da mutane 108 da ta kama da laifuka daban-daban a yayin zanga-zangar a gaban kotu kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar DSP Dungus Abdulkarim ya bayyana.

A jihar Kano ma an kama jimillar mutane 632 saboda zargin lalata kadarori a lokacin zanga-zangar.

An bayyana za a gurfanar da mutanen a gaban kotu a ranar 19 ga Agusta.

Masu zanga-zangar a Kano sun fasa manyan shaguna saye da sayarwa, ginin Hukumar Sadarwa ta Kasa da ke Sakatariyar Audu Bako, kona ababan hawar jama'a tare da lalata fitilun kan tituna da bambare kwalta.

A jihar Gombe ma a ranar Asabar an sallami masu zanga-zanga 14 daga cikin 111 da aka kama karkashin kotun musamman da babbar alkaliyar jihar Halima Mohammed ke jagoranta.

Ana ci gaba da tsare da sauran mutane 97 wadanda ake sa ran za su bayyana a gaban kotu a ranakun Talata da Laraba masu zuwa.

A jihohin Katsina, Niger, Kaduna, Borno da babban birnin Abuja ma an kama wasu masu zanga-zangar, wadanda an kai wasu kotu, ana jiran kai wasun su a makon nan.

A ranar 1 ga Agusta ne 'yan Nijeriya suka fara zanga-zangar neman kawar da mummunan shugabanci a kasar.

TRT Afrika