An buɗe rumfunan zaɓe da misalin ƙarfe 7 na safe a agogon ƙasar inda fiye da mutum miliyan tara suka yi rajistar zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki./ Hoto: TRT Afrika

'Yan Rwanda suna kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa ranar Litinin, wanda ake sa rai Shugaba Paul Kagame mai shekara 66, da ya kwashe shekaru 24 a kan mulki, zai sake yin nasara.

An buɗe rumfunan zaɓe da misalin ƙarfe 7 na safe a agogon ƙasar inda fiye da mutum miliyan tara suka yi rajistar zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki. Ana sa ran sanar da sakamakon zaɓen ranar 20 ga watan Yuli.

A kan tituna, galibin mutane sun ce za su zaɓi Kagame wanda suke jinjinawa saboda ayyukan ci gaba da yake yi a ƙasar mai mutum miliyan 14 bayan kisan kiyashin da ta faɗa a ciki a shekarar 1994.

"Kagame ya yi mana ayyuka sosai... muna da tsaro, 'ya'yanmu suna zuwa makaranta, kuma ana ba su abinci," a cewar Tuyiringirimana Olivier, wani birkila wanda ke zaune a lardin kudancin Rwanda.

An hana 'yan adawa tsayawa takara

"Wannan shi ne ya sa za mu sake goyon bayansa. Tuni na bayyana aniyata kan hakan. Ina da ƙwarin gwiwar cewa Rwanda tana kan hanyar ci gaba."

Kagame, wanda ya jagoranci wata ƙungiyar 'yan tawaye da ta ƙwace mulki bayan kisan kiyashin 1994, ya zama shugaban ƙasa 2000. Yana fafatawa ne da 'yan takara biyu, Frank Habineza da Philippe Mpayimana, waɗanda suka fafata da shi a zaɓen shekarar 2017.

An haramta wa 'yan takara da dama tsayawa takara, cikinsu har da wasu fitattun masu sukar salon mulkin Kagame, inda aka zarge su da laifuka daban-daban.

Kagame ya samu nasara da kimanin kashi 99 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen 2017, wanda aka gudanar bayan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar da ya kai ga cire wa'adin shugaban ƙasa.

TRT Afrika