Tsohon mai taimaka wa Buhari ya ce an biya Rarara kudin dukkan wakokin da ya yi wa tsohon shugaban Nijeria./Hoto:Other

'Yan Nijeriya sun kaure da muhawara sakamakon kalaman da fitaccen mawakin nan na Hausa, Dauda Kahutu Rarara ya yi wadanda wasu ke gani a matsayin butulci ga tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Rarara, wanda ya yi fice wajen goyon baya da kare gwamnatin Buhari a lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023, ya gudanar da taron manema labarai ranar Alhamis a Kano inda ya bijiro da batutuwa da dama ciki har da rawar da ya taka wajen nasarar jam’iyyar APC a zaben 2023.

Ya bayyana cewa yana sahun gaba a cikin wadanda suka taimaka wa APC domin kuwa idan ban da mutane irin su "Kashim Shettima da Nuhu Ribadu da Abdullahi Ganduje da kuma Aminu Bello Masari babu wanda ya fi ni."

Rarara ya bayyana takaicinsa na ganin "mutanen da suka yaki Bola Tinubu" amma yanzu suna cikin gwamnatinsa, yana karawa da cewa ba zai zuba ido yana ganin hakan na faruwa ba kamar abin da a cewarsa ya faru lokacin Buhari.

Ya ce, "Ba za mu yi irin hakurin talakawa da Buhari ba. Ka san hakurin talakawa da Buhari a karshe dalma ya zuba musu...ka san me ye dalma? Canjin kudi...

"Sun kasa fitowa su fada wa mutane gaskiya...Buhari sai da ya kashe kasar nan. Buhari ya yi dama-dama da kasar nan.”

Ya ce lokacin da suka karbi mulkin kasar daga hannun jam’iyyar PDP a shekarar 2015, “mun fito mun fada an ce kasar a kashe take. Dalilin da ya sa mutane suka rika yi wa Buhari uzuri kenan. Me ya sa mu yanzu za mu boye?”.

Kazalika mawakin ya ce gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari samun nasara, inda ya kara da cewa “wata ukun da Tinubu ya yi, sun fi shekara takwas da Buhari ya yi.”

"Akwai hankali a maganarsa?'

Sai dai tuni mutane suka rika mayar da martani kan sukar da mawakin ya yi wa Muhammadu Buhari.

Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, ya yi tambaya cewa anya akwai hankali a kalaman Rarara?

Ya ce bai so yin martani a kan kalaman ba, amma tun da Rarara ya ce ko Buhari bai taimaki kansa kamar yadda shi ya taimake shi ba, shi ya sa yake gani akwai alamar tambaya a cikin maganarsa.

Ya ce, "Na farko, cikin bidiyon, Rarara ya yi ikirarin cewa wai gudunmawar da ya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai ba wa kansa irin wannan gudunmawa ba. Ikon Allah. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana?

"Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a ba shi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a ba wa mukaman na ministoci. Tashin hankali. Ko akwai chemistry, balle technology a cikin wannan batu?"

Jaafar Jaafar, dan jarida mawallafin jaridar Daily Nigeria, ya wallafa ra’ayinsa kan batun a shafinsa na Facebook yana cewa; “Matsalar Rarara ita ce: bai sani ba, kuma bai san bai sani ba.”

“Rarara ya yi butulci gaskiya. Toh, ko me ya sa ya yi irin wannan batu oho,” in ji Abubakar Barde.

Farfesa Ibrahim Malumfashi, malamin jami’a a Nijeriya, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a fashinsa na Facebook.

Ya ce, “Kuskuren da yawancin ake yi game da batun Rarara bai wuce ana yi masa kallon maroki ko mawaki ba ne kurum!

“Wasu kuma na ganin ai bai ma da ilimi ko mutanen da zai iya bugun gaba da su, a ce ya zama wani abu a jam'iyyar APC ko siyasar Nijeriya.

“Kuskure ne a ɗauki irin wannan mutum da baiwar da Allah ya yi masa da tasirin da baiwar take da shi a farfajiyar zamantakewa da siyasar Arewacin Nijeriya, a matsayin ɗan ƙauyen Kahutu da ya samu dama, wanda cikin kusan shekara 15 ya zama ɗan ma'abban da ke naɗa Sarki da muƙarrabansa,” in ji Farfesa Malumfashi.

A cewarsa: "Kuskure ne a yi tunanin cewa ba zai iya juya lamura da baiwarsa a yanzu ba, kamar yadda ya yi a baya."

TRT Afrika