Dokar kasar ta nemi a yanke hukuncin kisa kan laifuka da dama ciki har da cin amanar kasa./Hoto: Ghana Parliament Facebook

'Yan majalisar dokokin Ghana sun kada kuri'ar soke hukuncin kisa a kasar, abin da ya sa ta bi sahun wasu kasashen Afirka da suka yi watsi da hukuncin na kisa.

'Yan majalisar dokokin sun jefa kuri'ar ne ranar Talata.

Da ma dai babu wanda aka zartar wa hukuncin kisa a Ghana tun 1993 duk da yake akwai mutum 176 da aka yanke wa hukuncin ya zuwa shekarar da ta wuce, a cewar hukumar kula da gidajen yari ta kasar.

A bara an yanke wa mutum bakwai hukuncin kisa a Ghana - amma ba a zartar da ko daya ba. Dokar kasar ta nemi a yanke hukuncin kisa kan laifuka da dama ciki har da laifin cin amanar kasa.

Dan majalisar dokoki Francis-Xavier Sosu ne ya gabatar da kudurin gyara ga dokar kisa ta kasar kuma ya samu goyon bayan kwamitin majalisar dokokin da ke kula da harkokin tsarin mulki da dokoki da sha'anin majalisa.

Wata kungiya da ke rajin ganin an soke hukuncin kisa a duniya mai suna Death Penalty Project (DPP), wadda ta hada gwiwa da Mr Sosu don ganin an soke hukuncin na kisa, ta ce Ghana ce kasar Afirka ta 29 da ta soke hukuncin kisa, sannan ita ce ta 124 a duniya.

A shekarun baya-bayan nan, kasashen Afirka da dama sun soke hukuncin kisa, wadanda suka hada da Benin, Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Chadi, Equatorial Guinea, Saliyo da Zambia.

TRT Afrika da abokan hulda