'Yan bindiga sun kashe fararen hula 10 tare da raba mutane da dama da muhallansu a wani hari da suka kai kan al'ummar Amegu Nkalaha a ƙaramar hukumar Ishielu da ke jihar Ebonyi a yankin kudu maso gabashin Nijeriya, a cewar 'yan sanda a ranar Litinin.
Maharan, waɗanda aka yi amannar 'yan ƙungiyar aware ta IPOB ce, sun kuma cinna wa gidaje da dama wuta tare da lalata dukiyoyi, kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda Joshua Ukandu ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu.
Ukandu ya ce "An ƙona gidaje da dama a wasu yankunan sannan an lalata kadarori. Bayan da muka samu labarin ne sai muka aika 'yan sanda wajen."
Yawan hare-hare
"A yanzu haka muna bincike kan lamarin yayin da abubuwa suka dawo daidai a yankin," ya ƙara da cewa.
Kudu maso gabashin Nijeriya na fama da hare-hare daga ƙungiyar ta 'yan bindiga da ke fafutukar ɓallewa daga Nijeriya don kafa ƙasar Biafra.
A shekarun 1960 ma an yi irin wannan fafutukar wadda ta zama silar ɓarkewar yaƙin basasar da aka ƙiyasta cewa an kashe mutum miliyan ɗaya.
Dakarun tsaron Nijeriya na ta ƙoƙarin daƙile ƙungiyoyin 'yan bindiga da dama da suka hada da na ta'addanci ta Boko Haram da na masu satar mutane da arewacin Nijeriya.