Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno.

A kalla mutane 40 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe a jihar Borno da ke Arewa maso-gabashin Nijeriya, in ji wani babban jami'in gwamnatin jihar a ranar Litinin.

Ana zargin wani ɓangare da ya ɓalle daga ƙungiyar ta Boko Haram da ke biyayya ga 'yan ƙungiyar IS ne ya kai harin a ranar Lahadin da ta gabata a garin Dumba na jihar Borno, in ji gwamnan jihar Babagana Umara Zulum.

Gwamnan ya gargaɗi fararen hula da su kasance a yankunan da suke da tsaro inda sojoji suka fatattaki 'yan ta'adda da ɓata gari daga cikin su, inda ya kuma yi kira ga jami'an soji da su gudanar da bincike game da harin.

"Ina son na tabbatar wa 'yan jihar Borno cewa za a binciki wannan batu sosai tare da ɗaukar matakan da suka kamata. Ina son amfani da wannan dama na yi kira ga rundunar soji da ta kamo tare da hukunta wadanda suka kai harin mai muni kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba," in ji shi.

Ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram mai iƙirarin jihadi a Nijeriya, sun ɗauki makamai a 2009 don yaƙi da gwamnati da kuma neman aiwatar da shari'ar Musulunci. Rikicin ya zama mafi daɗe wa a tarihin Afirka, wanda ya tsallaka zuwa maƙotan Nijeriya ta iyakar arewacin ƙasar.

Majalisar DInkin Duniya ta bayyana cewa tun daga 2014 zuwa yanzu an kashe fararen hula kimanin 35,000 a arewa maso-gabashin Nijeriya.

TRT Afrika da abokan hulda