'Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike kan wannan hari. Hoto/Reuters

Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa ‘yan bindiga sun sace wasu ‘yan jarida biyu da iyalansu a Jijar Kaduna.

‘Yan bindigar sun afka unguwar Ɗanhonu da ke Millennium City a jihar inda suka afka gidajen ‘yan jaridar inda suka sace su da matansu da ‘ya’yansu, kamar yadda jaridar Daily Trust a Nijeriyar ta ruwaito.

Rahotannin sun ce ‘yan jaridar da aka sace, Alhaji AbdulGafar Alabelewe wanda ma’aikacin gidan jaridar The Nation ne da kuma AbdulRaheem Aodu, wanda ma’aikacin gidan jaridar Blueprint ne dukansu na zaune a unguwa ɗaya.

Alhaji Alabelewe shi ne shugaban ƙungiyar ‘yan jarida masu ɗauko rahoto reshen jihar ta Kaduna.

Wani ɗan uwan AbdulGafar wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa ɓarayin sun afka cikin unguwar ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar Asabar inda suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi kafin gudanar da aika-aikar.

Ya bayyana cewa sun sace Alhaji Alabelewe da matarsa da ‘ya’yansu biyu, inda shi kuma Alhaji Aodu suka sace shi da matarsa sai dai sun bar ɗiyarsa maras lafiya.

“Da farko, sun sace Alhaji AbdulGafar da matarsa da ‘ya’yansa uku da wata yarinya da ke zama da su kafin suka umarci yarinyar ta koma da ɗaya daga cikin yaran, wanda hakan ya sa aka tafi da AbdulGafar da matarsa da ‘ya’yansa biyu.”

“Sun lalata ƙofofin, da tagogi sun cire ƙarafan taga bayan sun haura katanga.”

Wani ɗan uwan Mista Aodu ya bayanna cewa a lokacin da ɓarayin suka zo, sun ɓalle ƙofar gidan inda suka ɗauke shi da matarsa sai dai sun bar ‘yarsa wadda ba ta da lafiya.

Zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ba ta yi ƙarin bayani dangane da wannan harin da ‘yan bindiga suka kai ba.

TRT Afrika da abokan hulda