Shugaban Jami'ar ya ce an sace daliban ne a wajen makaranta yayin da aka sace wasu ma'aikatan gine-gine a cikin Jami'ar./Hoto: Reuters

Hukumomi a jihar Zamfara ta arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun sace dalibai da dama na Jami'ar Tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar.

Shugaban Jami'ar Farfesa Mu'azu Abubakar ya tabbatar wa TRT Afrika aukuwar lamarin, sai dai bai fadi adadin daliban da aka sace ba.

Ya ce an sace dalibai da wasu ma'aikata ne ranar Alhamis da maraice zuwa Juma'a da safe a cikin makarantar da kuma gidajen kwanan dalibai a unguwar Sabon Gida da ke kusa da Jami'ar.

"Lamarin ya faru ne tun karfe takwas (ba ma da daddare sosai ba) har zuwa karfe biyar na safe maharan nan na yin abin da suka ga dama a ciki da wajen Jami'ar nan," in ji Farfesa Abubakar.

Shugaban Jami'ar ya ce an sace daliban ne a wajen makaranta yayin da aka sace wasu ma'aikatan gine-gine a cikin Jami'ar.

"A cikin gari aka dauki daliban ba a makaranta ba. Amma an dauki wasu ma'aikatan gine-gine a cikin makarantarmu, kuma 'yan bindigar sun wargaza dukkan Jami'ar," a cewar Farfesa Abubakar.

Ya kara da cewa kawo yanzu an kubutar da mutum shida kuma ana ci gaba da bin sahun sauran da aka sace.

Jihar Zamfara ta dade tana fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wadanda kan sace dalibai da mutanen gari,

A watan Fabrairun 2021, masu garkuwa da mutane sun sace daibai mata fiye da 300 daga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe.

TRT Afrika