An kashe fararen hula 21 a makon da ya gabata yayin wani hari da aka kai kan ayarin motocin jigilar kayayyaki a kusa da Tera.   / Hoto: AA

An kashe fararen hula 21 a makon da ya gabata yayin wani hari da aka kai kan ayarin motocin jigilar kayayyaki a kusa da Tera, a yammacin Nijar, yankin da ake yawan fuskantar hare-haren mutane masu dauke da makamai, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a karshen mako.

Gidan rediyon gwamnati Voix du Sahel ya tabbatar da cewa an kai harin ne a mahadar iyakar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

"Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wa motocin da ke dawowa daga kasuwar mako-mako a Tera hari a ranar 5 ga watan Disamba, a yankin mai tazarar kilomita 12 a arewa da Tera, kusa da Bankilare," in ji shi.

Sojojin Nijar na kai hare-hare da dama kan kungiyoyin jihadi a yankin Tillaberi, inda ake alakanta wadannan hare-hare da "yan ta'adda."

AA