Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta ce dole gwamnatin ƙasar ta janye ƙarin da ta yi na kuɗin lantarki,/Hoto:OTHER

Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya inda suka durƙusar da harkoki daban-daban.

Tun kafin asubahi ne dai NLC ta katse babban layin wutar lantarki na Nijeriya lamarin da ya jefa dukkan ƙasar cikin duhu, a cewar kamfanin da ke rarraba hasken lantarki na ƙasar (TCN).

"An katse babban layin wutar lantarkin ne da misalin ƙarfe 2.19 na safe, ranar 3 ga watan Yunin 2024," in ji sanarwar da kakakin kamfanin TCN, Ndidi Mbah ya fitar ranar Litinin.

Hakan na faruwa ne a yayin da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago ta NLC da TUC a Nijeriya ta sha alwashin tsunduma yajin aiki tare da kassarar harkokin ƙasar domin tursasa wa gwamnatin Bola Tinubu ta riƙa biyan ma'aikata aƙalla N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Ganawar da shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar wakilai Tajedeed Abbas suka yi da wakilan 'yan ƙwadagon ranar Lahadi ta gaza shawo kan yunƙurin shiga yajin aikin.

"Da misalin ƙarfe 1:15 na safe, masu raba lantarki na Tashar Lantarki ta Benin sun ce an kori ma'aikatan tashar, kuma an doki ma'aikatan da suka ƙi fita sannan aka jikkata wasu daga cikinsu a yayin da ake tursasa musu fita daga ɗakin kunna lantarki, lamarin da ya sa wuta ta ɗauke baki ɗaya," a cewar TCN.

Tun kafin asubahi ne dai NLC ta katse babban layin wutar lantarki na Nijeriya lamarin da ya jefa dukkan ƙasar cikin duhu, a cewar kamfanin da ke rarraba hasken lantarki na ƙasar (TCN).

Sauran tashoshin rarraba lantarki da ƙungiyar ƙwadago ta rufe su ne Ganmo, Benin, Ayede, Olorunsogo, Akangba da Osogbo, in ji sanarwar.

Kazalika ƙungiyar kwadagon ta tilasta rufe tashar rarraba lantarki ta Jebba da wasu ƙananan tashoshin lantarki.

"Da misalin ƙarfe 3.23 na safe, TCN ta soma yunƙurin dawo da lantarki inda ta yi amfani da babbar tashar lantarki ta Shiroro domin samar da hasken lantarki a ƙaramar tasha da ke Katampe, Matsalar ita ce har yanzu ƙungiyar ƙwadago tana ci gaba da kawo tarnaƙi a faɗin Nijeriya," a cewar TCN.

Tsaiko a jigilar jiragen sama a Lagos

Kazalika yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi a Nijeriya ya kawo cikas a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed da ke Lagos, babban birnin kasuwanci.

Fasinjoji sun shaida wa manema labarai cewa ba a bar su sun shiga inda jirage ke tashi ba saboda yajin aiki.

An rufe ma'aikatu, kotuna da bankuna a Kano

A jihar Kano da ke arewacin ƙasar, 'yan ƙungiyar sun rufe makarantu da ma'aikatu da bankuna har ma da kotuna a yunƙurinsu na tabbatar da tasirin yajin aikin.

Wakilin TRT Afrika Hausa ya ce lamura sun fuskanci tsaiko, ko da yake wasu kasuwannin sun buɗe domin gudanar da harkokinsu.

TRT Afrika